Kevin de Bruyne ya taimaka wa Man City wurin zura kwallo 11  a matakin sili-daya-kwala na gasar cin Kofin Zakarun Turai. Hoto/Getty

Kevin De Bruyne ya ceto Manchester City daga hannun Real Madrid bayan da ya farke kwallon da aka zura musu a zagaye na farko na wasan kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun yi fafatawar ce a filin wasa na Santiago Bernabéu inda suka tashi da ci 1-1.

Dan wasan Real Vinicius Jr ne ya soma zura kwallo a minti na 36.

Yaran Pep Guardiola sun taka rawar gani a farkon wasan inda sau biyu golan Madrid Thibaut Courtois ya hana De Bruyne, Rodri da Erling Haaland yunkurin zura kwallo.

De Bruyne ya zura wa City kwallonta ne a minti na 67 lamarin da ya yayyafa ruwa a zukatan 'yan Man City.

City na sane cewa idan ta yi nasara a kan Madrid a zagaye na biyu ranar Laraba mai zuwa za ta samu gurbin zuwa wasan karshe na biyu a tarihi inda za ta fafata da Inter Milan ko AC Milan.

Yanzu dai City ta buga wasa 21 a dukkan gasa ba tare da an yi nasara a kanta ba, inda ta yi galaba a wasa 17.

TRT Afrika da abokan hulda