Robinho haziƙin ɗan wasan Brazil ne a baya. / Hoto : AFP

An kama tsohon ɗan wasan Manchester City da Real Madrid, Robinho, a Brazil, bayan ya yi rashin nasara a kotu kan yunƙurin jinkirta fara zaman gidan yari na shekaru tara da aka yanke masa, saboda yi wa wata mata fyaɗe shekaru goma da suka wuce.

Alƙalin Kotun ƙoli, Luiz Fux ya yi watsi da roƙon da Robinho ya gabatar na a jinkirta aiwatar da hukuncin, inda ya zartar da cewa, "umarnin tsarewar ya ci gaba da aiki..., don ya fara zaman gidan yarin da aka yanke masa."

Rundunar ƴan sandan Tarayyar Brazil a birnin Santos da ke kudu maso gabashin ƙasar ta ce jami'anta "sun zartar da umarnin kame Robson de Souza, wato Robinho."

"Fursunan zai fuskanci gwajin likita a (Cibiyar Medical Legal Institute), sai kuma jin bahasi a gidan yari, sannan za a tura shi ya fara zaman kaso," cewar ƴan sandan a wata sanarwa da suka miƙa wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Alhamis da daddare.

Zaman gidan kaso

A 2017 wata kotun Italiya ta samu Robson de Souza wanda ya yi suna da "Robinho," da laifin kasancewar ɗaya daga cikin gungun mutanen da suka yi wa wata mata ƴar Albania fyaɗe, yayin da take bikin cika shekara 23 da haihuwa a wani gidan rawa da ke Milan, shekaru huɗu gabanin nan.

Tsohon ɗan wasan na Brazil, wanda yake da shekaru 40 yanzu, ya yi rashin nasara a ɗaukaka ƙarar da ya yi a 2020, sannan kotun ƙolin Italiya ta jaddada hukuncin a 2022. Bayan nan ne masu shigar da ƙara suka shelarta sammacin kama shi.

Kasancewar Brazil ba ta amicewa ta miƙa ɗan ƙasarta ga hukomomin ƙasashen waje, Italiya ta nemi a maimakon haka Robinho ya yi zaman gidan kaso a ƙasarsa ta haihuwa.

Wata kotu a babban birnin ƙasar, wato Brasilia ta amince ranar Laraba, da ƙuria tara-da-biyu, sannan ranar Alhamis, shugabar kotun Maria Thereza de Assis Moura ta rattaba hannu kan takardar da ta ba damar ba da sammacin garƙame Robinho.

Mace cikin maye

Daga nan ne lauyoyin Robinho suka shigar da ƙara a Kotun Ƙoli don neman ka da a kama shi har sai an kammala shari'ar da yake ƙalubalantar hukuncin. Amma an ƙi amincewa da hakan.

Ɗan wasan wanda ke iƙirarin bai aikata laifi ba, ya faɗa wa wani gidan talabijin, mai suna TV Record a wata tattaunawa da aka yi ranar Lahadi cewa, tarawar da ya yi da matar da amincewarta ne, kuma ya zargi mahukuntan Italiya da nuna bambancin launin fata.

A cewar zargin, Robinho da sauran mutanen da ake zargi sun sanya matashiyar ta sha barasa, "har sai da ta gusar da hankalinta yadda ba za ta iya ƙin amincewa ba" sannan suka "yi layi suna ta yin lalata da ita".

Gazawar hukumomi

A watan Maris na 2021, kotun ɗaukaka ƙara a Milan ta sami Robinho da laifin nuna "ƙasƙantawa ga matar da ya zalunta, wadda ta kunyata matuƙa."

Shari'ar Robinho da kuma ta Dani Alves, wanda shi ma ɗan Brazil ne, ta haifar da suka kan cewa hukumomin ƙwallon ƙafa a Brazil sun gaza yin alla-wadai da cin mutuncin mata.

A watan Fabrairu, an yanke wa tsohon ɗan wasan baya na Brazil, Dani Alves mai shekara 40, hukuncin zaman shekaru huɗu da rabi a gidan yari, sakamakon yi wa wata mata fyaɗe a wani gidan rawa da ke birnin Barcelona na Sifaniya.

TRT Afrika da abokan hulda