Frank Lampard ya ce ba ya tsammani zai iya warware matsalolin da suka addabi Chelsea a kwana daya bayan sun sha kashi a hannun Wolves ranar Asabar.
Wolves ta doke Chelsea da ci 1-0 a wasan farko da Lampard ya jagoranta sakamakon sake nada shi a matsayin kocin kungiyar fiye da shekara biyu bayan an kore shi daga aiki.
The Blues sun gaza yin nasara a wasa uku a jere a yayin da suka sha kashi sau 11 a kakar wasa ta bana.
Kai Havertz, Raheem Sterling da Joao Felix ba su taka rawar gani ba, yayin da himmar da Enzo Fernandez, Kalidou Koulibaly da Wesley Fofana suka yi ta hana jefa wa kungiyar karin kwallaye.
Lampard ya ce akwai "gagarumin aiki" wurin warware matsalolin Chelsea."
"Muna sane cewa ba wannan matsayin ne ya dace da mu ba. Akwai dalilai da dama da suka sanya haka. Ba na sa ran warware kowacce matsala a rana guda," in ji Lampard.
Sai dai ya kara da cewa akwai bukatar su sake jajircewa domin samun nasara.
"Ya kamata 'yan wasan su san da hakan domin kuwa idan ba ka jajirce ba ba za ka yi nasara a wasa ba. Na san cewa akwai zakakuran 'yan wasa kuma na zo nan ne domin na taimaka," a cewar Lampard.
A makon jiya ne aka sake nada Lampard a matsayin kocin Chelsea bayan sallamar tsohon manajanta Graham Potter sakamakon kashin da suka sha a hannun Aston Villa.