Foden da Shaw sun lashe kyautar kungiyar marubuta ta Football Writers’ Association

Foden da Shaw sun lashe kyautar kungiyar marubuta ta Football Writers’ Association

Foden, mai shekara 23, ya ci kwallaye 24 kuma ya taimaka an ci kwallaye 10 a wasanni 50 da ya buga wa Manchester City.
Phil Foden

An bayyana ‘yan wasan Manchester City biyu Phil Foden da Khadija Shaw a matsayin wadanda suka lashe kyautar marubuta ta Football Writers’ Association ta bana.

Foden, mai shekara 23, ya ci kwallaye 24 kuma ya taimaka an ci kwallaye 10 a wasanni 50 da ya buga wa Manchester City.

Dan wasan gaban na Ingila ya samu kuri’u 42 cikin 100 a bangaren maza, inda ya doke Declan Rice wanda ya zo na biyu da kuma takwaransa dan Man City wato Rodri a matsayi na uku.

Kyaftin din Arsenal Martin Odegaard da dan wasan gaban Aston Villa Ollie Watkins da kuma dan wasan Chelsea Cole Palmer su ne suke sauran matsayi na shida.

Foden wanda aka haifa a Stockport shi ne dan wasan Man City na uku a shekaru hudu da ya lashe kyautar. Erling Haaland ya taba lashewa a shekarar 2023 da Ruben Dias wanda shi ma ya taba lashewa a shekarar 2021.

“Ina matukar farin cikin da na lashe wannan kyautar,” in ji Foden. “Yanzu zan mayar da hankali na kammala wannan kaka da karfina yayin da nake kokarin taimaka wa City ta lashe kofin.”

Kadijia Shaw, mai shekara 27, ita ce ta fi kowace ’yar wasa da ta fi zura kwallaye a raga a Gasar Women Super League. Kuma ita ce ta lashe a bangaren mata.

TRT Afrika da abokan hulda