Tashin da aka yi canjaras ya jefa Croatia cikin hatsari sakamakon za a iya waje da ƙasar a matakin rukuni. / Hoto: Reuters

An tashi 2-2 a wasan da aka kara tsakanin Albania da Croatia a Gasar Euro 2024 a ranar Laraba.

Tashin da aka yi canjaras ya jefa Croatia cikin hatsari sakamakon za a iya waje da ƙasar a matakin rukuni.

Klaus Gjasula ya ci gidansa Albania a bisa kuskure a minti na 76 sai dai a lokutan ƙarshe na tashi wasan ya samu nasarar ci wa ƙasarsa ƙwallo domin wanke laifinsa.

Bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Sifaniya da ci 3-0 a wasansu na farko, Croatia na a baya a lokacin da Qazim Laci ya ci wa Albania ƙwallon farko a Hamburg.

Sai dai Croatia ta farfaɗo a wasan bayan da ta sauya ‘yan wasa biyu, inda Andrej Kramaric ya rama ƙwallon wanda hakan ya ja suka zama kunnen doki.

Bayan minti biyu da haka sai Gjasula ya ci gidansa Albania bisa kuskure. Sai dai ɗan wasan tsakiyar na Albania ya zama gwarzo a ƙarshen wasan ana dab da tashi wanda hakan ya ja suka tashi canjaras.

Ƙasar Croatia, wadda ta kai zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Euro 2022, akwai buƙatar ta ci wasan da za ta buga da Italiya a ranar 24 ga watan Yuni idan har tana so ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale.

AFP