Nasarar da Real Madrid ta samu kan Villarreal a Asabar ɗin nan, ta dakushe sakamakon raunin da haziƙin ɗan wasansu mai tsaron baya, Dani Carvajal ya samu ana dab da ƙare wasan.
An ji kururuwar Carvajal yayin da ya yi kwance a filin wasa yana riƙe gwiwarsa, bayan gwiwar ƙafarsa ta yi karo da cinyar ɗan wasan Villarreal, Yeremy Pino a minti na 90 da ƙari na wasan da Madrid ta yi nasara da ci 2-0.
'Yan wasan madrid sun zagaye Carvajal wanda yake ta rusa kuka, inda jami'an lafiya suka shigo suka ɗauke shi cikin gadon majinyata, suka fita da shi daga filin wasa na Santiago Bernabeu.
Sai dai bayan tararrabin jiran labarin munin raunin da Carvajal ya samu, 'yan awanni kaɗan an ga ya wallafa saƙo a Instagram, inda ya nuna hotonsa cikin motar ɗaukar mara lafiya, kuma ya tabbatar da nau'in raunin da ya samu.
Carvajal ya faɗa cewa, “An tabbatar da raunin tantanin ƙasan gwiwa. Za a yi min tiyata kuma zan bar buga wasan na 'yan watanni. Ina fatan farfaɗowa kamar toro. Ina godiya ga saƙonninku, na ji matuƙar ƙaunar da kuka nuna mini.”
'Yan wasa da masoya Real Madrid suna jajanta raunin da haziƙin ɗan wasan nasu ya samu, kasancewa akwai jerin manyan 'yan wasansu da suke fama da jinya a halin yanzu.
Cikin masu jinyar akwai David Alaba, ɗan wasan baya, mai jinyar tantanin gaɓa, Brahim Diaz, ɗan wasan tsakiya, mai jinyar babbar jijiya, Dani Ceballos, ɗan wasan tsakiya, mai jinyar agara, da Thibaut Courtois, babban mai tsaron raga, mai jinyar jijiyar gaɓa.
Dani Carvajal yana da shekaru 32 a duniya, kuma ya taimakawa Real Madrid lashe kofuna da dama tsawon zamansa a ƙungiyar, wadda a yanzu take mataki na biyu a LaLiga a ƙasan Barcelona.
Rashinsa zai iya samar da giɓi a ƙarfin tawagar da Carlo Ancelotti ke jagoranta, da ma tawagar ƙasar Sifaniya da yake buga wa wasa.