Dan wasan tsakiya na Mexico Edson Alvarez / Hoto: AFP

West Ham United ta sayi dan wasan tsakiya na Mexico Edson Alvarez daga Ajax kan kwantiragin shekaru biyar, a cewar sanarwar da kulob din ya fitar ranar Alhamis.

West Ham ba ta bayyana sharuddan da aka bi wajen sayen dan wasan ba amma Ajax ta ce kungiyoyin biyu sun amince da cinikin mayar da dan wasan zuwa West Ham a kan Yuro miliyan 38 (dala miliyan 41.90), adadin da ka iya karuwa zuwa Yuro miliyan 41 zuwa gaba.

"Mun yi matukar farin ciki da saka Edson a cikin 'yan wasanmu," in ji kocin West Ham David Moyes bayan sa hannunsa na farko a yarjejeniyar musayar 'yan wasa ta bazara.

"Dan wasan tsakiyar shi ne wanda muke so mu fi mayar da hankali a kansa a wannan lokaci na bazara kuma Edson zai kara wa sauran ‘yan wasan da muke da su a sashen.

"Gogaggen dan wasan kasa da kasa ne, wanda ya samar da gagarumin nasara ga kungiyar da yake taka wa leda da kuma kasarsa tun tasowarsa a harkar wasan kwallo zuwa yau," a cewar David Moyes.

Dan wasan, mai shekaru 25, wanda ya sa hannu a kwantiragin buga wa Ajax wasa har zuwa 2025, ya kasance zakaran kasar Holland sau biyu, kuma ya buga wasanni 147.

Ya zura kwallaye 13 a dukkan gasannin da ya buga wa kulob din Eredivisie tun lokacin da ya fara wasa a kungiyar a shekarar 2019.

Ya buga wa Mexico wasa har sau 69, ciki har da gasar cin Kofin Duniya ta 2018 da 2022.

Zuwansa West Ham zai kara wa kungiyar, wacce ta sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice wa Arsenal, a kan fam miliyan 105 a wani ciniki na musaya tsakanin kungiyoyin Birtaniya biyu.

TRT Afrika