Dan wasan Norway Erling Haaland ya zura kwallonsa ta 35 a Gasar Firimiya a kaka daya a wasan da Manchester City ta koma saman tebirin gasar bayan ta doke West Ham da ci 3-0.
Kwallon da Haaland ya jefa a ragar West Ham ta ba shi damar karya tarihin da Alan Shearer da Andrew Cole suka kafa na cin kwallo 34 kowannensu a kakar wasan firimiya daya.
Da ma dai Haaland ya karya tarihin da Mohamed Salah ya kafa inda ya ci wa Liverpool kwallo 32 a kakar wasa ta 2017-18.
Yanzu shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar firimiya kuma yana da sauran wasa biyar kafin karshen kakar bana.
Nathan Ake da Phil Foden ne suka ci sauran kwallo biyun.
'Yan wasan kungiyar da kocinsu Pep Guardiola sun yi masa jinjinar ban girma bayan an kammala wasan a filin wasa na Etihad.
Haaland ya shaida wa Sky Sports cewa "wannan dare ne na musamman kuma lokaci ne na musamman. Ina matukar farin ciki da alfahari."
Yanzu City na da maki 79 da kuma sauran wasa daya yayin da Arsenal ke biye mata da maki 78.