Joao Cancelo  ya taimaka wa Manchester City ɗauƙar kofin Zakarun Turai na 2023 da kuma kofunan Premier uku na Ingila./Hoto: OTHER

Ɗan wasan baya na Manchester City ɗan ƙasar Portugal Joao Cancelo ya koma ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya a ranar Laraba, bisa ga kwantiragin shekara uku, a cewar ƙungiyar.

"Ƙungiyar Al-Hilal, ƙarƙashin jagorancin 'Mista Fahad Bin Saad Bin Nafel', ta kammala sayen ɗan wasan ƙasar Portugal Joao Cancelo daga 'Manchester City' ne domin ya taka leda da tawagar ƙwallon ƙafa ta Al-Hilal na tsawon kaka uku," kamar yadda wata sanarwa ta Al-Hilal ta bayyana.

"An gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata, a otal din 'Four Seasons George V' da ke babban birnin ƙasar Faransa Paris, a gaban shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar," in ji sanarwar.

Ko da yake dai, ba a bayyana takamaiman nawa ne kuɗin kwangilar ba.

Cancelo, mai shekaru 30, ya buga wasa a manyan ƙungiyoyin Turai da suka haɗa da Benfica da Valencia da Barcelona da Inter Milan da Juventus da kuma Bayern Munich.

Ɗan wasan ya koma Man City ne a shekarar 2019 daga Juventus, inda ya lashe kofunan gasar Premier uku a jere daga shekarar 2021 zuwa 2023 bayan da ya samu nasarar lashe gasar Seria A da Juve a shekarar 2018 zuwa 2019.

Ya kuma taimaka wa Portugal lashe gasar UEFA Nations League ta 2019.

Kazalika ɗan wasan na Portugal ya taimaka wa Manchester City ɗauƙar kofin Zakarun Turai na 2023 da kuma kofunan Premier uku na Ingila.

Reuters