Xavi ya kara da cewa 'yan wasansa suna kokari kamar yadda ya dace / Hoto: AFP

Kocin Barcelona Xavi Hernandez ranar Litinin ya ce lokacin da yake dan wasa a kungiyar an sa wani tsari mai inganci wanda a yanzu ake kokarin ganin an kiyaye shi a gasar ta Zakarun Turai.

Barca ta dauki kofuna hudu a dukkan gasa da aka yi daga 2006 da 2015, sannan ta fuskanci wulanci a wasu lokuta.

Barcelona ta sha kashi a hannun Roma da Liverpool da kuma Bayern Munich a shekarun baya-bayan nan, yayin da suka gaza kai wa matakin rukuni a kakar wasanni biyu da suka wuce.

"Akwai matsin lamba sosai a kanmu, saboda an riga an daga darajar kungiyar -- wannan ita ce Barca," in ji Xavi a taron manema labarai.

"Wannan shi ne tasirin da Barca ta yi a shekaru kadan na baya, a zamanin da muke 'yan wasa. A shekara 10 da suka wuce, daga 2006 zuwa 2015, mun lashe kofi hudu na Zakarun Turai."

Kocin ya ce manufar kungiyar ita ce su yi nasara a matakin rukuni, gabanin wasansu na farko da za su fafata da kungiyar Royal Antwerp ta Belgium ranar Talata.

"Muna son kalubale, amma burin da ake da shi a kanmu yana da matukar yawa, yana da nauyi," in ji shi.

"Hakan ya faru ne saboda gadon da muka yi na abubuwan alheri da kwazo, na kafa tarihi mafi kyawu a kungiyar nan."

Sai dai Xavi ya kara da cewa 'yan wasansa suna kokari kamar yadda ya dace kuma yana murnar soma gasar Zakarun Turai ta bana.

"Idan na kalli fuskokin 'yan wasan, ina ganinsu cike da murna da fata na gari," a cewar Xavi.

Barcelona bata kashe kudi da yawa wajen sayen 'yan wasa a bazara ba saboda tana fama da karancin kudi, ko da yake ta sayi 'yan wasa irin su Joao Felix da Joao Cancelo a mataki na aro.

AFP