A ƙarshen kakar wasannin da ta gabata, Guardiola ya bayyana cewa har yanzu yana ɗaukar Ederson a matsayin zaɓinsa na farko / Hoto: AP

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ba zai iya tabbatar da ko Ederson zai ci gaba da zama a ƙungiyar ba a bazarar nan.

Mai tsaron ragar ɗan ƙasar Brazil na cikin 'yan wasan da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Saudiyya ke nema.

A ƙarshen kakar wasannin da ta gabata, Guardiola ya bayyana cewa har yanzu yana ɗaukar Ederson a matsayin zaɓinsa na farko, duk da cewar ya zaɓi Stefan Ortega a wasan farko na fafatawar da suka yi a wasan kwata-fainal da Real Madrid.

Da yake bayani bayan shan kaye a hannun Celtic a North Carolina da ci 4 da 3, Guardiola ya bayyana cewa “Zan so ya zauna amma ya danganta da sauran ƙungiyoyi.”

Ya ƙara da cewa “Ban san yanayin da ake ciki ba. Babu wata ƙungiya da ta tuntuɓe mu a ‘yan kwanakin. Batu ne na samun horo, zai iya kasancewa tare da mu har nan da ƙarshen kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa sannan za mu gani.”

TRT Afrika da abokan hulda