Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya yi fatali da maganar da wasu ke yi cewar kungiyar tana cikin matsala, yana mai cewa kungiyar tana bin tafarkin da ya dace.
United ta samu galaba a kan Chelsea ta hanyar kwallayen da Scott McTominay ya zura a raga kuma wasa ya tashi 2-1 – karon farkon a wannan kakar da yaran Ten Hag suka doke wata kungiyar da ke cikin goma na farko a teburin firimiya.
Kocin na United ya ce kungiyarsa ta samu karin tagomashi.
Ten Hag ya yi murna da sakamakon wasansu na baya-bayan nan sai dai ana ganin ya shiga tashin hankali bayan shan kaye a Newcastle.
"Tashin hankali? Ba ma cikinsa," in ji shi. "Hankalinmu a kwance yake. Kulob din yana tafarkin da ya dace.
"Ba takaici ba ne, amma da mun kara kaimi [ta hanyar cin karin kwallaye ]," in ji shi.