Kocin Arsenal ya ce yana da yakinin za su yi nasara a kan Liverpool a wasan ranar Lahadi duk da cewa sun shafe tsawon shekaru ba su yi nasara kan kungiyar a Anfield ba.
Arsenal na gaban Manchester City da maki takwas a teburin Gasar Firimiya gabannin wasannin da za a kara a karshen mako, inda ‘yan wasan na Pep Guardiola za su fafata da Southamptom, wadda ke kasan teburin a ranar Lahadi.
Rabon da Arsenal ta yi nasara a Anfield tun lokacin da Arteta yake taka leda inda ya buga wani wasa da Arsenal din ta ci 2-0 a 2012.
A karkashin jagorancin Jurgen Klopp, Liverpool ta ci wasanni shida da kulob din ya buga da Arsenal da cin kwallaye da suka kai 22-4 a jumullar wasannin.
Sai dai a halin yanzu Liverpool din tana gararamba a matsayi na takwas a kan teburi, inda take bayan Arsenal da maki 29, haka kuma Arsenal ta cimma burin da ta dade take son cimmawa na lallasa Tottenham a gidansu.
“Kulob dinmu ya kagara kuma yana da yakini kan abu mai kyau kuma mun san muna da babban kalubale a gabanmu amma kuma akwai babbar dama ta zuwa Anfield tare da yin wani abu da ba mu taba yi ba tsawon shekaru,” kamar yadda Arteta ya bayyana a hira da manema labarai kan batun wasan da ke tafe.
“Mun san abin da ya kamata mu yi. Mun yi wasa a wurare mafi wahala,” in ji shi. Kwallaye biyun da Gabriel Jesus ya ci a wasan da aka tashi 4-1 da Arsenal din ta doke Leeds a makon da ya gabata ya kara ba Arteta kwarin gwiwa.
Wasan da Saka ya buga din shi ne wasansa na farko tun Nuwamba sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita,