Raunin da Havertz ya ji zai hana shi wasa har zuwa ƙarshen kakar bana. / Hoto: Reuters

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ɗora alhakin raunin da ɗan wasansu na tsakiya, Kai Havertz ya yi a matsayin 'babbar matsala'.

"Babbar matsala ce saboda yawan masu jinya da muke da shi. Mun samu 'yan wasa da suka ji rauni bayan sun buga wasanni 130 a kaka biyu da suka gabata, don haka haɗari ne da aka san zai faru idan ka ci gaba da tara musu aiki," in ji Arteta.

Arteta ya ƙara da cewa doguwar jinya ta Kai Havertz a wannan makon ta ƙara wa Arsenal matsala kan jerin 'yan wasanta da ke jinya ba sa buga wasa.

An tabatar da girman raunin da Havertz ya ji ne ranar Alhamis, wanda zai hana shi wasa har zuwa ƙarshen kakar bana.

Tawaga mai jinya

Arsenal ta ce za a yi wa ɗan wasan ɗan asalin Jamus tiyata don gyara jijiyar bayan gwiwarsa wadda ta samu lahani yayin atisaye a Dubai a makon jiya.

Havertz ya ji raunin ne lokacin da ya miƙe ƙafarsa don tare ƙwallo, kuma hakan ya haifar wa Arsenal rashin wani babban ɗan wasa gaba bayan Gabriel Jesus ya tsinka ACL ɗnsa a watan jiya.

Baya ga Havertz da Jesus, Arsenal ta rasa Bukayo Saka, Gabriel Martinelli, da Takehiro Tomiyasu a wasan da za su buga ranar Asabar a gasar Firimiya a gidan Leicester.

Yawaitar wasa

"Muna jin dadin kasnacewar mu a sansanin Dubai, sai kawai ciwon ya afku ta hanyar da a atsammata ba, kuma wannan babban kalubale ne saboda ciwukan da muke da su," in ji Arteta.

Manajojin kwallon kafa daban-daban sun sha neman 'yan wasa da su rage yawan ayyukansu, wanda aka dora laifin hakan kan yawan ciwukan da suke samu a wasanni.

A watan Satumban 2023 Pep Guardiola ya ce bijirewar 'yan wasa ce kadai za ta sanya masu ruwa da tsaki a harkokn kwallon kafa su rage yawan wasanni a kasakar wasanni don rage wahalar da 'yan wasa ke sha.

TRT Afrika