Wannan ne karon farko da Arsenal ta yi nasarar doke Man City a gasar Firimiya cikin shekara takwas.
Tun bayan da Arsenal ta yi nasarar doke Man City da ci daya da nema ne dai mutane suka soma bayyana ra’ayoyinsu game da nasarar da yaran Mikel Artetat suka yi kan yaran Pep Guardiola.
Wasu masharhanta na ganin wannan nasarar na nufin Arsenal za ta iya kwace kofin gasar Firimiya daga hannun Manchester City a lokacin da za a karkare gasar a watan Mayu mai zuwa.
Duk da cewa kwallon da Martinelli ya buga ya sha karkata kafin ya shiga ragar Man City, ana ganin wannan nasarar za ta kara wa Gunners karfin gwiwa.
Idan za su iya sauya tarihin nasarar da City take yi na shekara takwas, me zai sa Gunners ba za su iya sauya tarihinsu na rashin cin kofi na shekara 20 ba?
Ana ganin baya ga ƙara wa Arsenal ƙarfin gwiwa, wannan nasarar da Gunners suka yi kan City za ta iya nuna wa Tottenham da ke saman teburin Firimiya yanzu da ma Liverpool cewa ƙungiyar Pep Guardiola za ta iya shan kaye idan aka yi amfani da jajircewa da kuma dabarar da ta dace.
Wasu ma na ganin wannan nasarar ta nuna cewa kowa ma zai iya dauke kofin gasar firimiya, ba Manchester City kadai ba.
Wannan nasarar ta bai wa Mikel Arteta damar doke kulob din da ya yi wa aikin mataimakin koci a karon farko bayan ya kasa samun ko maki daya a karawa bakwai kungiyarsa ta yi kungiyar tsohon abokin aikinsa Pep Guardiola.
Mikel ya cimma wannan nasarar ne duk da cewa dan wasan gaban da yake ji da shi Bukayo Saka bai buga wasan ba, kuma daya tauraronsa, Martinelli bai iya fara wasan daga farko ba.
Dabarun da Mikel ya yi amfani da su sun taimaka domin Gunners sun hana City yin shot din da ya zarce hudu, abin da ba a taɓa musu ba cikin shekara 13.
Sai dai kuma masharhanta na tambaya game da rashin iya zura ƙwallo a raga da dan wasan gaban Man City, Erling Haaland ya yi a wasan duk da cewa dan wasan ya kasance dan wasan gaba da aka fi jin tsoro a Gasar Firimiya.
Amma wasu na ganin City ta yi kewar dan wasan Sifaniya Rodri wanda ya samu jan kati a karawar City da Nottingham Forest.
Masu wannan ra’ayin na ganin City ta sha kaye a karawarta da Newcastle da Wolves da kuma Arsenal, wasannin da Rodri bai buga ba.