Har yanzu dai Arsenal ce ta biyu a teburin gasar Firimiya. Hoto/Getty Images

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayar da hakuri ga magoya bayan Arsenal bayan rashin nasarar da kulob din ya yi a wasansu da Brighton. Brighton ta je har gidan Arsenal din inda ta lallasa ta da ci 3-0.

“Muna jin wani iri idan aka kwatanta da yadda muka ji a Lahadin da ta gabata [a wasa da Newcastle] a lokacin da muka yi murna muka kuma ji cewa mun yi iya yinmu domin samun nasara a lokacin.

Yau dai abu ne daban ya same mu. “Akwai bukatar mu bai wa mutanenmu hakuri saboda gazawarmu, musamman ma bayan hutun rabin lokacin da aka je,” in ji Arteta.

“Mun yi iya kokarinmu domin kawowa inda muke a yanzu kuma a yau mun shiga wani irin hali, inda muke ci gaba da fatan cimma burinmu,” in ji shi.

Idan Arsenal din ta yi rashin nasara a wasan da za ta yi da Nottingham Forest ranar Asabar, Manchester City za ta zama wadda ta yi nasara a gasar ta Firemiya.

Masoya Arsenal dai sun yi ta nuna takaicin yadda aikin Arsenal yake rushewa yayin da aka zo karshen kakar gasar ta bana. Arsenal dai ta ja ragamar teburin makonni kusan talatin, kafin baya-bayan nan da damar daga kofin na Ingila yake subuce mata.

A halin yanzu dai Manchester City ce kan teburin gasar yayin da Arsenal ke bin ta a baya. Sa’annan, New Castle da Manchester United na biye da su a mataki na uku da na hudu.

Kuma wasannin biyu ne dai suka rage kafin a kammala gasar Firimiya, inda idan Arsenal ta kuskure daukar kofin, Man City za ta daga shi a karo na uku a jere.

Da ma dai an sha yi wa masoya Arsenal gori, da cewa kulob din ba shi da laka ko alkadari.

TRT Afrika da abokan hulda