Tsohon zakaran damben boksin na duniya ajin babban nauyi Anthony Joshua ya soma dawowa da martabar wasansa bayan ya doke dan wasan damben Amurka Jermaine Franklin sau biyu a jere a Landan a ranar Asabar.
Damben wanda aka kara shi a gaban yan kallo 2000 shi ne wanda dan damben mai shekara 33 ya kara yi tun bayan da ya sha duka a hannun zakaran Ukraine mai kambunan WBA da IBF da WBO da IBO wato Oleksandr Usyk.
Haka kuma wannan ne kuma karon farko da ya samu nasara a dambe a sama da shekara biyu, wanda hakan ke nufin a tarihin dambensa ya yi nasara sau 25 an kuma yi galaba a kansa sau uku.
Alkalai ukun da suka yi alkalancin damben bakinsu ya zo daya a irin makin da suka bayar wanda hakan ya kai Joshua ga yin nasara.
Makin da da suka bayar shi ne 118-111 da 117-111 sai kuma 117-111.
Ga Franklin kuwa mai shekara 29, wannan ne karo na biyu da ake doke shi bayan da Briton Dillian Whyte ya yi nasara a kansa a Nuwamba.
Irin naushin da Joshua ya soma kaiwa da farko da alamu ba su da wani karfi, wanda hakan ya sa Franklin mai shekara 29 ya soma samun karfin gwiwa, inda har ya rinka gwalo ga abokin damben nasa wanda ya fi shi tsawo.
Joshua, wanda jini ya rinka fitowa daga hancinsa tun da farkon fara damben, amma duk da haka shi ya yi nasara.