A Disamban 2023 ne Ancelotti ya sabunta kwantiraginsa da Real Madrid duk da tawagar kasar Brazil ta so ɗaukar sa. / Hoto: AP

Haziƙin kocin ƙwallon ƙafa a duniya, Carlo Ancelotti ya shiga kakarsa ta ƙarshe a Real Madrid, kamar yadda bayanai ke nuna cewa zai ajiye aiki idan an kammala kakar wasa ta bana.

Rahotannin na cewa Ancelotti ya yanke hukuncin barin Real Madrid a ƙarshen kakar 2024-25, duk da cewa yana da kwantiragi da ƙungiyar har zuwa 2026.

A watan jiya ne, Ancelotti mai shekaru 65 a duniya ya kafa tarihin zama kocin da ya fi kowanne yin nasara a ƙungiyar Real Madrid, lokacin da ya ciyo wa ƙungiyar kofi na 15 sanda ya ci kofin Nahiyoyi na duniya da aka a yi Qatar.

Wani rahoto na Onda Cero ya bayyana cewa dattijon kocin yana farin cikin kasancewa a kulob ɗin, amma ya zartar da hukuncin cewa zai bar Madrid bayan wannan kaka.

Sai dai ana cewa da wuya idan kocin zai yi ritaya da horar da ƙungiyar ƙwallo ko da ya bar Real Madrid.

Tsohon ɗan wasan Madrid, Xabi Alonso, wanda a yanzu yake jagorantar Bayer Leverkusen har ta ci kofin Bundesliga na bara, shi ake yawan ambatawa a matsayin wanda zai gaji Ancelotti.

A yanzu dai, Ancelotti zai ci gaba da mayar da hankali wajen ganin Real Madrid ta samu kofunan lashewa a bana, inda ranar Laraba zai fuskanci RB Leipzig a gasar Zakarun Turai.

TRT Afrika