Carlo Ancelotti ya hora da kungiyoyin ƙwallo a ƙasashe daban-daban. / Hoto: AFP

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya faɗi ra'ayinsa game da yadda gasar La Liga ta bambanta da gasar Firimiya wa ɓangaren taka wasa.

An tambayi Ancelotti, wanda ya kasance daya daga cikin shahararrun koci-koci da suka lashe kofuna da dama a Turai, game da abin da ya bambanta manyan gasannin Turai guda biyu.

An yi masa tambayar ne bayan wasan da Real Madrid ta buga da Celta Vigo inda ta yi gagarumar nasara ranar Lahadi. Ancelotti wanda ɗan asalin Italiya ne ya ci kofuna da dama a duka gasannin biyu.

Ancelotti ya ce, "Tabbas suna da bambanci, amma hakan ba ya nufin wani ya fi kyau ko wani ya fi muni ba. Kawai dai a matakin nuna dabarun ƙwallo, La Liga ta yi nesa da gasar Firimiya ta Ingila."

"Amma idan ana zancen zafin wasa, ta nuna iya taku, gasar ta Ingila tafi ta Sifaniya. Amma tabbas La Liga ta fi inganci wajen nuna hikimar buga ƙwallo," in ji Ancelotti.

Dattijon kocin yana magana ne a lokacin da kulob ɗin da yake jagoranci a yanzu yake kan gaba a teburin La Liga, bayan ya ƙara ba da tazara ga kulob ɗin da ke biye masa, wato Girona, bayan doke Celt Vigo da ci 4-0.

Carlo Ancelotti shi ne koci ɗaya tilo da ya taɓa cin kofin gasar ƙasa a duka manyan ƙasashen Turai, kasancewar ya lashe kofi da Chelsea, da AC Milan, da PSG, da Real Madrid, da kuma Bayern Munich.

Wasan Real Madrid na gaba, Ancelotti zai jagoranci kulob ɗin inda za su kara da Osasuna a gasar La Liga ramar 16 ga Maris. Wasan zai zo ne bayan an je hutun wasannin ƙasa-da-ƙasa ranar 31 ga Maris.

TRT Afrika