Cole Palmer ya ci ƙwallaye uku wanda ya sa Chelsea ta cinye wasan. / Hoto: Getty Images

Cole Palmer ya ci ƙwallaye biyu ana dab da ƙare wasa inda ƙwallayensa suka kai uku, har ta kai ga Chelsea ta ba wa Manchester United mamaki ta doke ta da ci 4-3 a daren Alhamis.

Tawagar Man United ƙarƙashin koci Erik ten Hag ta nuna alamun nasara bayan da suka juya akalar wasan daga sanda ake cinsu 2-0, suka dawo suna jan wasan da ci 3-2.

Amma sai ana dab da ƙare wasan sai Cole Palmer ya sake juya akalar wasan inda ya zura ƙwallo ta hanyar bugun ɗurme a minti na 100, sannan ya dawo ya ƙara zura ta huɗu wadda ta ba wa Chelsea nasara a wasan da aka buga a gidanta da ke Stamford Bridge.

Manchester United ce ke da ci 3-2 har zuwa minti na 99 da sakan 17, wanda shi ne maƙurar lokacin da wani kulob ya kai yana nasara a wasan da a ƙarshe ya yi rashin nasara a tarihin gasar Firimiya.

Ci mai zafi

Sakamakon wasan ya janyo Man United tana tsaye a mataki na shida, inda maki 11 ya raba ta da Aston Villa wadda ke mataki na huɗu, yayin da wasanni takwas kacal suka rage a kammala gasar ta Firimiya.

A yanzu Chelsea ƙarƙashin koci Mauricio Pochettino ta kai mataki na 10 a tebur, inda hakan zai ba ta damar ci gaba da neman shiga cikin ƙungiyoyi biyar na saman tebur, don su iya buga gasannin Turai a baɗi.

Pochettino ya ce 'yan wasansa sun fara da ƙarfi, amma zura musu ƙwallaye biyu da aka yi a farkon wasan "ya so ya kashe musu gwiwa".

Kocin wanda ɗan Argentina ne da ke kakarsa ta farko a jagorancin Chelsea, ya yaba wa Cole Palmer ɗan shekara 21, wanda ya daɗe yana wa kulob ɗin ƙoƙari tun sanda ya shigo a watan Satumba.

Da sauri-sauri

Kafin buga wannan wasan Chelsea ba ta yi galaba kan Manchester United ba a cikin wasanni 12 na gasar Firmiya, amma a wannan wasan cikin sauri a minti na huɗu ta samu haye wa kan United ta hannun kyaftin Conor Gallagher.

Palmer ya ciyo ƙwallo ta biyu da bugun ɗurme a minti na 19, bayan da Anthony ya kayar da Marc Cucurella.

Amma United ta fara farfaɗowa a minti na 34 lokacin da Moises Caicedo ya yi sakacin sakin ƙwallon da Alejandro Garnacho ya samu ya tafi da ita ya zura a raga.

Minti biyar bayan nan, sai Diogo Dalot ya ba da ƙwallo ga Bruno Fernandes, wanda ya saka mata kai ta shige raga.

Haka wasa ya tafi a zango na biyu na wasan, har lokacin da Garnacho ya ci ƙwallo da kai, bayan da Antony da bugo ta, inda United ta haye sama a minti na 67.

Alamu sun nuna United na za su yi galaba amma sai jami'an wasan suka ce za a ƙara mintuna takwas kafin kammalawa.

Farfaɗowa

Chelsea ta samu farfaɗowa bayan da Dalot ya far ma Noni Madueke inda rafali Jarred Gillett ya yanke hukunci a filin wasan na bayar da bugun ɗurme, kuma alƙalin VAR ya tabbatar.

An yaba wa Cole Palmer da ƙoƙarinsa a wasan. / Hoto: Getty Images

Sai dai ba a nan zancen ya are ba domin kuwa ana 3-3 sai Chelsea ta shammaci United inda Enzo Fernandez ya tura wa Palmer wata ƙwallo mai kyau.

Shi kuwa Palmer ya daki ƙwallo inda ta tsere wa Andre Onana duk da sai da ta doki Scott McTominay na United, inda Chelsea ta haye sama kuma masoya suka ɗauki shewa a filin wasan na Stamford Bridge.

Zuwa yanzu dai Palmer ya ci ƙwallaye 19 tun bayan zuwansa a ranar 1 ga watan Satumbar bara.

Wanna wasa ya zo wa Manchester United da rashin sa'a. Kuma a yanzu abin da za su mayar da hankali shi ne wasansu na gasar FA tare da Coventry a zagayen kusa da ƙarshe.

Shi kuwa kocin United Ten Hag, yana shan matsin lamba a kakar wasansa ta biyu a kulob ɗin, yayin da sabon mamallakin kulob ɗin Jim Ratcliffe yake tunanin ci gaba da aiki da Ten Hag ko sauya shi.

TRT Afrika da abokan hulda