An yi wa ɗan wasan gaban West Ham Michail Antonio tiyata bayan ya samu “karaya a ƙafarsa” sakamakon hatsarin mota, kamar yadda kulob ɗin nasa ya tabbatar a ranar Lahadi.
Hatsarin motar ya rutsa da ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Jamaica ne a wajen birnin Lanadan a ranar Asabar, inda bayan nan aka garzaya da shi asibiti.
“Za a ci gaba da kula da Michail a asibiti a kwanaki masu zuwa,” kamar yadda West Ham ɗin ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
“Kowa a kulob din na yi wa Michail fatan samun lafiya cikin gaggawa tare da mika godiyarsa ga masoya ƙwallon ƙafa baki daya bisa ga gagarumin goyon bayan da aka nuna tun bayan samun labari a jiya, tare da mika sakon godiya ga jami’an bayar da agajin gaggawa da kuma waɗanda suka bayar da agaji a farko ga Michail a cikin gaggawa bayan faruwar lamarin, da kuma tawagar likitocin da ke ci gaba da taimaka masa wajen samun sauki."
Wasu hotuna da ba a tabbatar da sahihancinsu ba waɗanda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta sun nuna wata mota ƙirar Ferrari wadda ta yi matuƙar dameji. Babu tabbaci ko a cikin motar ne ɗan wasan mai shekara 34 ya yi hatsarin.
Antonio ya soma taka leda a West Ham tun a 2015 inda ya yi wa ƙungiyar wasa fiye da 300.