'Yan wasan da ke wakiltar Nijeriya a gasar Olympics da ke gudana a birnin Paris, waɗanda ke gasar tseren ba da sanda ta maza, ba za su ci gaba da shiga wasan gaba na gasar ba.
An soke damar 'yan wasan huɗu da suka haɗa da Emmanuel Ojeli, Ezekiel Nathanial, Dubem Amene, da Chidi Okezie, ta shiga gasar maza ta mita 400 sau 4 a ranar Juma'a.
Tawagar ta maza ta ƙare wasan dab da na ƙarshe na gasar ta mita 400 sau 4 a mataki na biyu, kan tsawon lokaci da ya kai 2:59.81, wanda ya ba ta damar shiga wasan ƙarshe.
Sai dai a yanzu alƙalin wasa ya soke cancantar tawagar Nijeriya, saboda ɗaya cikin 'yan wasan ya shiga da'irar ɗan wasan Afirka ta Kudu a yayin karɓar sanda.
Sakamakon wannan hukunci, tawagar Afirka ta Kudu ce za ta maye gurbin ta Nijeriya wajen shiga wasan ƙarshe na gasar.
Sauran ƙasashen da za su shiga wasan ƙarshen su ne Botswana, Birtaniya, Amurka, Japan, Faransa, Belgium, Zambia, Italiya, da Afirka ta Kudu.