Ezinne Kalu ta ciyo maki uku sau huɗu kuma ta ci maki 17 cikin 19 a rabin lokaci na farko ranar Litinin, yayin da Nijeriya ta ci wasanta na farko a Gasar Olympic na wasan ƙwallon kwando na mata, wanda rabonta da nasara tun 2004 a birnin Athens, inda ta doke Australia da ci 75-62 a wasansu na farko a matakin rukunin.
Nijeriya ba ta samu cancantar zuwa gasar da ta gudana a 2016 a Rio Games ba, kuma a gasar da aka yi a birnin Tokyo ba ta yi nasara ba.
Australia na ƙarƙashin koci Sandy Brondello daga ƙungiyar New York Liberty ta Amurka, kuma tagarta ta zo a matsayi na uku a duniya, inda Nijeriya take matsayi na 12.
Masoya da ke filin wasa na Pierre Mauroy Stadium sun yi kuruwar murna da jinjina wa Nijeriya a daƙiƙoƙin ƙarshe kafin 'yan wasa da kocin sun dumfari tsakiyar filin don murna. Daga nan suka tafa da 'yan Australia.
Promise Amukamara ta ƙara maki 14 ga Nijeriya, sai Amy Okonkwo da ciyo maki 13 sannan Murjanatu Musa ta samo maki 11.
Nijeriya ta matsa gaba, inda sakamako ya kai makin 24-22. Kalu, wadda aka haifa a birnin Newark, jihar New Jersey, kuma take wasa a Savannah State, ba ta kuskure ba har sai a bugunta na biyar, lokacin da ya rage minti 1:24 a zagaye na biyu.