Fitaccen ɗan wasan harbi na Turkiyya Yusuf Dikec ya yi wani harbi da ya sa ya samu shahara a Gasar Wasannin Olympics ta 2024, inda ya harba bindigar da hannu ɗaya a yayin da ɗaya hannun ke cikin aljihu, kuma labarin ya yaɗu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta.
Ya ɗauki kambin azurfa ba tare da amfani da kowane irin kayan aiki na ƙwarewa ko gilashi na musamman ba. A yanzu batun sa ya sake karaɗe shafukan sada zumunta bayan 'yar gajeriyar tattaunawarsa da Elon Musk da dubban mutane suka so.
"Barka dai Elon, kana ganin a can gaba mutum-mutumi za su iya samun nasara a Gasar Olympics yayin da hannunsu ɗaya ke sunne a cikin aljihu? Yaya batun tattauna hakan a Istanbul, babban birnin al'adu da ya haɗa nahiyoyi biyu?" ya tambayi Musk.
Shugaban babban kamfanin fasahar mazaunin Amurka ya mayar da martani da gargaɗi cewa: "A koyaushe mutum-mutumi za su harbi tsakiyar wajen da ake so ɗin kai tsaye."
Sai dai nan da kuma sai Musk ya sake wallafa saƙo a X cewa yana sa ran ziyartar Istanbul, yana mai cewa "yana ɗaya daga cikin manyan biranen duniya."
Ba wannan ne karo na farko da Dikec ya jawo hankalin Musk ba.
A lokacin da wani mai amfani da shafukan sada zumunta ya saka hoton Dikec da ya karaɗe shafukan sada zumunta, Musk ya yi sharhi da "da kyau" ɗan gasar harbi daga Turkiyya.
Rabon da Musk ya kai ziyara Turkiyya tun watan Nuwamban 2017, lokacin da ya gana da Shugaba Recep Tayyip Erdogan. Sun tattauna a kan batun samar da mota mai amfani da lantarki da makamashi mai ɗorewa.
A watan Satumban da ya gabata, Erdogan ya gana da Musk a Birnin New York, ya kuma gayyace shi Turkiyya to kafa kamfanin Tesla.
Musk ya amsa da cewa tuni Turkawa da dama suna aiki da Tesla kuma Turkiyya na daga cikin muhimman ƙasashen da za ta kafa kamfaninta nan gaba.
Yadda ya ci lambar yabo ta azurfa
Batun Dikec ya watsu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta saboda yadda ya yi gasar harbin a yanayi na ko oho, lamarin da ya kai shi ga nasarar samun kambin azurfa a Gasar Olympics ta 2024.
Hotunan da aka fi yaɗawa sun nuna Dikec yana yin harbin a yanayi na ko oho: cikin shigar riga T-shirt inda ya sunƙe hannu daya a cikin aljihun wandonsa, kuma sanye da madaidaicin tabarau na ƙara ƙrfin gani. An ba shi sunaye da yawa kuma mutane sun kwatanta shi da abubuwa da yawa.
Dikec ya samu lambar azurfa a gasar harbin bindigar daga nisan mita 10 tare da Sevval Ilayda Tarhan.
Yana sa ran zuwa Wasannin Bazara a 2028. "Ina fata na je gasa ta gaba a Los Angeles don in samu lambar zinare," in ji shi a makon da ya gabata.