An naɗa tsohon kocin Chelsea da Tottenham Hotspur Antonio Conte a matsayin sabon kocin Napoli kan kwantiragin shekara uku.
Kocin mai shekara 54 ya shafe shekara uku ba tare da yana aikin koci ba tun bayan da ya bar Hotspur a Maris ɗin 2023 inda ya shafe watanni 16 a can.
Duk da rashin nasarar da ya samu a can, Conte ya samu nasara a baya a rayuwarsa ta horaswa bayan da ya ci kofin Firimiya a Chelsea a kakar 2016-2017 da kuma kofin FA kafin aka kore shi a 2018.
“Napoli wuri ne mai muhimmanci a duniya. Ina cikin farin ciki da zan zauna a kan shuɗiyar kujera,”.
“Tabbas zan iya yin alkawarin abu daya, zan yi iyakacin kokarina don ci gaban kungiyar.” Haka kuma kocin na ƙasar Italiya ya jagoranci Juventus ta samu nasara a Serie A sau uku a jere, daga 2011 zuwa 2014.
Napoli wadda ta ci Serie A a karon farko a cikin shekara 33 a bara, ta sha wahala wurin ganin ta samu irin nasarar a bana sai dai ta ƙare a ta goma.