A yanzu Jay Emmanuel-Thomas yana buga wasa a Greenock Morton ta Scotland. / Hoto: Getty

Ana zargin tsohon ɗan wasan tsakiya na Arsenal, Jay Emmanuel-Thomas bisa yunƙurin fasa ƙwaurin tabar wiwi ta kimanin fam £600,000 zuwa cikin Birtaniya.

Shafin Goal.com ya ruwaito cewa jami'an hukumar yaƙi da manyan laifuka ta Burtaniya, NCA sun kama akwatunansa biyu ranar Laraba, ɗauke da kilo 60 na ƙwayoyi da aka shigo da su filin jrigin Stansted Airport daga birnin Bangkok na Thailand, ranar 2 ga Satumba.

An zargi Emmanuel-Thomas wanda ɗan Ingila ne mai shekaru 33, da laifin shigo da ƙwaya aji na B, kuma zai bayyana gaban kotun majistire ta Carlisle ranar Alhamis bayan an tsare shi a hannun 'yan sanda.

Hukumar ta NCA ta kuma kama tare da zargin wasu mata biyu yayin binciken, inda babban mai bincike na hukumar David Phillips ya ce, “NCA na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi Kula da Iyaka don tattaro waɗanda ke da hannu a safarar ƙwaya, ciki har da masu sufuri da wanda suka shirya laifin."

"Muna kira da duk wanda aka tunkara da shiga harkar fasa ƙwaurin duk wata haramtacciyar ƙwaya, to ya tuna cewa akwai sakamako mai haɗari.”

Emmanuel-Thomas ya kammala makarantar koyon ƙwallo ta Arsenal kuma ya buga wa ƙungiyar sau biyar.

Ya bar Arsenal a 2011 inda ya buga wasa a QPR, Ipswich Town, MK Dons, Livingston, Aberdeen, da kuma a Indiya tare da kulob ɗin Jamshedpur. Haka nan ya buga wa tawagar Ingila ta 'yan ƙasa da shekara 19.

A bazarar nan, Emmanuel-Thomas ya koma ƙungiyar Greenock Morton ta Scotland bayan ya bar Kidderminster Harriers.

TRT Afrika