Yanzu dan wasan ba zai fafata a karawar da za su yi da Hoffenham ranar Asabar ba/ Hoto: Bleacher Report Football

Bayern Munich ya dakatar da Sadio Mane sakamakon naushin da ya yi wa dan kulob dinsu Leroy Sane bayan sun sha kashi a hannun Manchester City.

Yanzu dan wasan ba zai fafata a karawar da za su yi da Hoffenham ranar Asabar ba.

Rahotanni sun nuna cewa Mane ya naushi Sane bayan City ya doke su da ci 3-0 a Gasar Zakarun Turai ranar Talata a Etihad.

Bayanai sun ce sai da aka raba ‘yan wasan biyu.

Mane da Sane ba su ce komai game da fadan da suka yi ba.

Kulob din ya ce ya dakatar da dan wasan Senegal ne saboda “rashin da’a” yana mai cewa za a kuma ci tarar sa.

TRT Afrika da abokan hulda