Carlos Alcaraz ya lashe gasar Wimbledon karon farko a tarihi bayan ya doke Novak Djokovic, wanda ya lase gasar sau bakwai.
Hakan na nufin Alcaraz ya hana Djokovic cika burinsa na kafa tarihin lashe kambin Grand Slam sau 24.
Alcaraz ya jajirce don ganin bai fita daga gasar a zagayen farko ba inda a zagaye na biyu ya ci kwallo 1-6, 7-6 (8/6), 6-1, 3-6, 6-4 bayan awa hudu da minti 42 suna fafatawa a filin wasa na Centre Court da ke Landan ranar Lahadi.
Wannan shi ne babban kofi na biyu na gasar da dan kasar Sifaniya mai shekara 20 ya lashe bayan ya ci gasar US Open a shekarar da ta wuce inda yanzu ya zama na uku a jerin matasa zakarun Wimbledon a ajin maza.
Wannan sakamakon ya jawo muhawara game da yiwuwar samun sabbin jini da za su karbe ragamar gasar, bayan wadanda ake yi wa lakabi da 'manya uku' Djokovic, mai shekara 36 ya sha kashi, sannan an yi wa Roger Federer ritaya yayin da aka ware Rafael Nadal gefe guda, watakila kuma dindindin.
Zakaran Australian Open da French Open Djokovic ya yi ta kokarin ganin ya kafa bajinta irin ta Federer ta lashe kofin Wimbledon sau takwas sannan ya yi kankankan da Margaret Court wadda ta ci Slams sau 24.
Alcaraz bai kai shekaru biyar a duniya ba lokacin da Djokovic ya soma lashe babbar gasar Australian Open a 2008.