Kyle Walker, dan wasan baya na Manchester City ya bayyana wa kulob dinsa aniyarsa ta sauya sheka a watan Janairun nan, inda rahotanni ke cewa an samu kungiyoyi masu burin daukarsa.
Walker, wanda dan Ingila ne ya sanar da daraktan wasanni na kungiyar, Txiki Begiristain cewa yana so ya koma taka leda a kasar waje.
A wasan da Man City ta buga na karshe ranar Asabar inda kungiyar ta doke Salford da ci 8-0 a gasar FA, ba a saka Walker ba kwatakwata.
A yanzu dai AC Milan ta Italiya tana kan gaba wajen samun damar dauko dan Walker, wanda ke da shekaru 34 a duniya, wanda kuma ya kusa komawa Bayern Munich a 2023.
Duk da cewa Walker na da kwantiragi a Man City wadda ba za ta kare ba har sai 2026, shafin ESPN ya ruwaito cewa Milan ta shirya ba shi kwantiragi zuwa 2027.
Guardiola ya ce ba ruwansa Da yake magana game da yiwuwar tafiyar Walker daga City, koci Pep Guardiola ya ce, "Yanzu batu ne na yadda kasuwa za ta kaya".
"Dan wasa ne mai hazaka da zafin jini, kuma idan ya saka idonsa a abu, ba a iya tare shi a baya. Babban dan wasa ne. Idan ya ci gaba da nuna kuzari zai buga kwallo har nan da shekara daya, biyu, uku, ko hudu”.
"Ni dai na sha fada koyaushe, idan yana so ya gwada sa’arsa a wani waje, kungiyarmu ma za ta gwada sa’arta, kuma shi ne zai yanke hukunci ba ni ba.
"Abubuwa sun sauya a kasuwa, kuma za a rufe ta idan lokaci ya yi. Kuma ni ban san me zai faru ba,” in ji Guardiola.
Kocin ya amsa cewa rashin tabbas game da makomar Walker ce ta sanya bai saka shi a wasansu da Salford ba, kuma ya ce babu tabbacin zai saka shi a wasan da za su buga da Brentford ranar Talata.