Zane mai nuna masana kimiyya suna aiki a sansanin da za a gina a duniyar Wata. Hoto daga NASA

A zuwa duniyar wata da NASA za ta yi nan gaba, tana da shirin share wuri ne don zama. Karkashin shirin Artemis, hukumar binciken samaniya ta Amurka tana shirya zaunar da mutane a can a karon farko kan duniyar da ba tamu ba.

Sai dai gina sansani a Duniyar Wata ba karamin aiki ba ne. Akwai bukatar janareton samar da lantarki, da motocin zirga-zirga, da masauki. Wannan ya sa masu ruwa da tsaki a harkar ke kokarin cimma wadannan bukatu.

Yayin zantawarsa da AFP, Neal Davis, ya ce “Wannan bakandamiyar aikin fasaha ne”. Shi ne babban injiniyan tsare-tsare na Lunar Terria Vehicle, a kamfanin binciken samaniya na Dynetics.

Kamfanin Dynetics ya fito da samfurin motar zirga-zirga a duniyar wata, a yayin bikin baje-kolin harkar sararin samaniya na Colorado Springs.

Jami’in NASA, Jim Free ya ce amma da alama ba za a “samu mazaunin dindindin a doron Wata ba”, sai bayan shirin Artemis na gaba, wato na bakwai zuwa sama.

Shirin Artemis 3, shi ne shirin farko na sauka a Duniyar Wata, ba zai faru ba kafin shekarun 2030.

Ya kara da cewa, sansanin zai kunshi sassa da dama, don barbaza hanyoyin bincike da samar da saukin sauka a duniyar.

Lantarki da sadarwa

Duk da nisan lokacin kaddamar da shirin, kamfanoni tuni suka fara neman sa'arsu. “Matakin farko shi ne sadarwa”, a cewar Joe Landon, shugaban kamfanin Crescent Space da ke karkashin Lockheed Martin.

“Yi la’akari da cewa idan ka shiga sabon gida, za ka fara neman waya ne da intanet.”

Kamfanin zai fara kafa tauraron dan’adam guda biyu, inda yake da burin zama kamfanin intanet da GPS a Duniyar Wata.

Mr Landon ya kiyasta cewa jarin kasuwar Duniyar Wata zai kai dala biliyan 100, cikin shekara 10 masu zuwa.

Kamfanin Astrobotic, yana da ma’aikata 220, daya ne daga cikin kamfanoni uku da NASA ta zaba don kera allon tara hasken rana na solar.

Dole a sanya allunan solar a tsaitsaye saboda a turken kudu na Wata, wanda shi ne wajen da ake fatan kafa sansanin saboda yana da kankararren ruwa, Rana tana lekowa ne kadan a saman duniyar.

Motoci

Samfurin motar zirga-zirgar kan Wata da NASA ta kaddamar. Hoto: NASA

Domin ayyukan binciken kimiyyarta, NASA ta nemi ‘yan cikin masana’antar binciken samaniya da su samar da mota wadda samanta a bude yake, mai cin mutum biyu, nan da 2028.

Ba kamar motar shirin Apollo ba, ana fatan motar ta iya aiki da kanta ba tare da dan sama jannati ba.

Wannan na nufin za ta iya jure tsananin sanyi na daren Duniyar Wata, wadda kan dauki makonni biyu, da kuma awon zafi da kan sauka ya kai har -170 Salshiyas.

Kamfanoni da yawa sun fara yin nasara

Kamfanin Lockheed Martin ya hada gwiwa da kamfanin motoci na General Motors, don dogaro kan kwarewar kamfanin kan kera mota mai amfani da lantarki, da motocin da ba a yi su don kwalta ba.

Dynetics, karamin kamfanin fasaha ne na katafaren kamfanin Leidos. Shi ma ya hada gwiwa da kamfanin Nascar.

Dusar Duniyar Wata wadda ake kira “regolith” tana haifar da babban kalubale saboda rashin gudanar ruwa ko iskar da ke mulmule tsakuwa, ya janyo kasar tana da kaifi tamkar gilashi.

NASA ba ta ambaci kamfanin da ta zaba ba tukuna.

A matakan dogon zango, NASA tana aiki da kamfanin binciken samaniya na Japan, JAXA, don kera motar da 'yan sama jannatin ciki ba za su bukaci sanya kayansu na musamman ba.

An sanya hannu kan shirin NASA na Artemis Accords ranar 3 ga watan Mayun 2023 a hedikwatar NASA a Washington, DC/Hoto: NASA

Mazauni

A karshe dai, ‘yan sama jannatin za su bukaci wurin da za su cire hula su ajiye, inda za su kira gidansu.

NASA ta ba da kwangilar dala miliyan 57.2 ga kamfanin da ke jihar Texas, mai suna Icon, wanda ya kware a fasahar ginin 3D, don kirkiro da fasahar da ake bukata don gina tituna da filin saukar jirgi kan Wata, da kuma mazaunin jama’a.

Tunanin shi ne a yi amfani da kasar Wata a matsayin abar sarrafawa. Sauran kamfanoni, kamar Lockheed Martin, suna kirkirar mazauni da za a iya buga wa iska don amfani.

Kirk Shireman, shi ne mataimakin shugaban shirin binciken sararin samaniya na kamfanin kera jirgin sama na Lockheed Martin.

Ya gaya wa AFP cewa, “Abin ban sha’awa shi ne za ka iya sauka da shi kan Wata, sannan a buga masa iska. Kuma yana da karin fadin iya daukar mutanen da za su rayu kuma su yi aiki a ciki.

A ciki za a samu dakunan kwana, da dakin girki, da dakin ajiye kayan binciken kimiyya, da sauransu. Duka za a kafa su a sagale, don a iya motsa shi.

Takamaimiyar manufar komawa Duniyar Wata karkashin shirin Artemis shi ne taimakawa NASA su shirya wa babban aiki mai dogon zango na zuwa Duniyar Mars.

Shireman ya ce, “Ko nawa za mu kashe don kirkirar wadannan na’urori a kan Wata, muna son su yi aiki ga Duniyar Mars.”

TRT World