Yadda Kalankuwar nuna kayayyakin ado na Dakar na bana ya kayatar

Yadda Kalankuwar nuna kayayyakin ado na Dakar na bana ya kayatar

Ana gudanar da bukin duk shekara inda ake baje-kolin kayan ado nau'i daban-daban.
Sama da madinka 20 na zamani na Sanagal ne suka baje-koli a wajen. Hoto: Dakar fashion week

Daga Charles Mgbolu

Bikin Nuna Kayayyakin Ado na Dakar na bana, wanda shi ne karo na 21 ya wakana a Tsibirin Gorée da ke daf gabar tekun Senegal, inda sama da masu hada kayayyakin ado ’yan asalin Senegal guda 20 suka baje kolinsu.

Bikin kalankuwar mai taken, “Kayayyakin da aka hada a Afirka domin mutanen duniya,” ya samu halartar masu hada kayayyakin ado daga Najeriya da Afirka ta Kudu da Congo da Cote d'Ivore da Morokko.

An shawarci masu hada kayayyakin su yi amfani da tsofaffin kayayyaki wajen hada sababbin kaya. Hoto: Dakar Fashion Festival

Fitaccen mai tallan kayan ƙawa, wanda shi ne ya assasa taron, Adama N’Diaya ya bayyana bikin a matsayin wata dama domin bayyana kwarewa da baje kolin kayayyakin ado da suke surka kirkire-kirkire da fasahar mutanen Afirka da cigaban zamani.

“A Afirka, ado na nuna abubuwa da dama. Kayyakin adon Afirka na nuna kirkira da fasaha da bambance-bambancen al’adu, kuma yana da kyau sosai,” inji N’Diaya a wajen bude taron.

Baki daga wasu kasashen Afirka suna bayyana kayayyakin adonsu. Hoto: Dakar Fashion Festival

Bikin kalankuwar wanda ya wakana a tsakanin 7 ga Disamba zuwa 10 ga Disamba, an yi amfani da shi wajen kaddamar da shirin, “Daurewar kayayyakin ado’ wanda aka tsara domin taimaka wa masu hada kayayyakin ado wajen dorewar sana’arsu.

Taron ya samu halartar fitattun mutane da kayayyakin ado daban-daban kamar su kayayyakin Lame dresses da bronze organza boubous da bazin da rigunan sanyi da aka dinka da tsofaffin kaya da kayatattun gyalulluka da sarkoki masu kyau da sauransu.

An hori masu hada kayayyakin su yi amfani da fasaharsu wajen adana al’adun Afirka. Hoto: Dakar fashion festival

“Ina alfahari da su…. Masu hada kayayyakin adon ne masu fasahar kirkirar sababbin abubuwa,” inji N’Diaye.

An hori masu hada kayayyakin adon su kasance ababen koyi nagari ga matasa masu tasowa a kasar, sannan uwa uba su taimaka wajen adana al’adun da kayayykin adon ya suke bambanta Afirka da sauran kasashen duniya.

TRT Afrika