Tare da kusan mabiya miliyan 35 a manyan shafukan sada zumunta na yanar gizo, babu tantama Tiwa Savage 'yar Nijeriya ta zama wadda ake tattaunawa a kan ta a ciki da wajen Afirka.
Kasancewar ta sananniya a fannin waka, jami'ar Kent da ke Ingila, makarantar da ta yi digiri ta ba ta digirin digirgir a girmamawa a fannin wake a watan Yuli, 2022.
Jami'ar ta ce an karrama mawakiyar mai shekara 43 ne saboda ta zama abar koyi a duniyar waje a duniya.
An haifi Tiwa Savage 'yar auta a wajen iyayenta da ke da yara hudu a birnin legas na kasuwanci da ke Nijeriya a ranar 5 ga Fabrairun 1980.
Iyayenta su ne Olanrewaju Savage da Cecilia Savage. Sunan da aka rada mata bayan haihuwarta shi ne Tiwatope Omolara Savage.
A lokacin da take da shekara 11, iyayenta sun koma Landan da zama.
Mawakiyar na kaunar waka tun tana karama, a wasu lokutan tana waka a coci. Daga baya aka saka ta a makarantar koyon waka a Landan.
A lokacin da take da shekara 16, wata kungiyar mawaka a babban birnin Birtaniya sun shigar da ita ayyukansu, inda ya sanya ta fara waka a kungiyance.
Mawakiyar, ta ci gaba da neman ilimi, daga baya ta kammala digiri a Fannin Nazarin Kula da Kasuwanci a Jami'ar Kent.
Bayan kudirce aniyar daukar waka a matsayin sana'a, Tiwa ta koma New York City da zama a farkon shekarun 2000, kuma ta hanyar mu'amala ta hadu da mawakan R&B da suka hada da Mary J. Blige, Blu Cantrell.
A 2007, lokacin tana da shekara 27 - Tiwa ta shiga kwas din koyon waka a kwalejin Waka ta Berklee da ke Boston.
Ta fada wa shafin yanar gizon kwalejin cewa tana daga cikin dalibai mafi yawan shekaru, amma tsarin ajujuwan ya sanya ta ji kamar tana da shekara 19.
Daga baya Tiwa ta yi aiki da mawaka da dama a Amurka. A 2010, ta hadu da Tunji Balogun da aka fi sani da Tee Biliz, kwararren mawaki a Amurka a wannan lokaci. Tunji ya ja ra'ayinta kan cewar ta je Nijeriya ta dinga waka saboda akwai damarmaki da yawa a fannin.
Tiwa ta dawo Nijeriya inda ta fara aiki da Tunji, mutumin da ya zama minjinta kuma manajanta a tsakanin 2013 da 2018. Wasu dalilai da suka gaza sasanta wa a kan su su janyo rabuwar auren a suke da yarinya 'yar shekara 8.
"Kele Kele Love" - wakar da aka saki shekaru 10 da suka wuce - ta zama silar shuhurar Tiwa a nahiya.
Sai kuma "Eminado", "Love Me", "Key To The City". "Ma Lo", "All Over", "Koroba" da sau ran su.
Tiwa ce wadda take tunanin ita ce
A Afirka, ta hada kai da Diamond Platnumz da ke Tanzania a wakar "Fire" da Sauti Sol da ke Kenya a wakar "Girl Next Door", da dai sauran su.
Tiwa ta lashe a kalla kambi 20 da suka hada da MTV Africa Music Awards da Channel O Music Video Awards.
Ta kafa tarihi a 2018, a lokacin da ta zama mace mawakiya ta farko d ata lashe kambin Best African Act a wajen gasar MTV Europe.
Rahotanni sun ce Tiwa na karbar dala $100,000 idan aka gayyace ta casu.
Baya ga waka, mawakiyar ta ce tana fatan a nan gaba za ta sake samun masoyi...