Wata mai busa sarewa ‘yar kasar Ireland ta kafa sabon tarihin busa sarewa na tsawon mintuna 20 a wajen bukin casun da aka gudanar a Tsaunin Kilimanjaro na Tanzania – tudu mafi tsayi a nahiyar Afirka – a wani bangare na gangamin neman tallafa wa masu fama da wata cuta da a Turance ake kira ‘cystic fibrosis’.
Siobhan Brady mai shekaru 24, ta samu wannan nasara a ranar Talatar da ta gabata a wajen wakoki da bushe-bushen gargajiya da na zamani na kasar Ireland, sannan an hada da wakar Ed Sheeran ta ‘Little Bird’ a wajen gasar.
Brady ce ke rike da kambin kidan harp da aka gudanar a Tsaunin Himalayan a shekarar 2018.
A makon da ya gabata ne ta je Tanzania da ‘yan tawagarta su 18 bayan daukar shekaru suna gwaji da samun horo a Ireland, kamar yadda Kungiyar Shirya Busa Sarewa ta sanar wa manema labarai.
Ta ce “Al’amari ne da ba za a iya mantawa da shi ba, nasara da fuskantar kalubale a lokaci guda, kuma a madadin ‘yan tawagata ina gode wa duk wadanda suka aiko da sakonni dage kusa da nesa.”
Waka da kidan da Brady ta yi sun hada da wakar Tanzania mai taken ‘Thank you Tanzania’.
Kakakin gwamnatin Tanzania Gerson Msigwa na daga cikin wadanda suka taya Msigwa murna.
An kai ga wannan gaci ta hanyar hada kai da tawagar da ke Afirka mai mambobi kusan 60.
Ana gadar cutar ‘cystic fibrosis’ da ke janyo daskarewar majina a kirji da huhun dan adam.