Shahararren mawakin Nijeriya Asake ya mayar da martani game da rashin nasarar da ya yi a karo na 66 na Gasar Grammy a watan fabrairu, inda shi da sauran manyan mawakan Nijeriya irin su Davido, Burna Boy da Ayra Starr suka sha kaye a hannun Tyla 'yar kasar Afirka ta Kudu.
An tsayar da Asake takarar neman lashe kambin Mawakin Afirka da Ya Fi Kowanne tare da wakarsa ta Amapiano da ya yi tare da abokinsa dan Nijeriya Olamide.
Asake ya shaida wa Mujallar Lifestyle GQ cewa ai nada shi a matsayin dan takarar neman lashe gasar ma ya isa.
"A waje na ba asara ba ce. Akwai yiwuwar na samu a shekara mai zuwa. Amma a kwakwalwata, ban wani damu sosai ba.
Na yada da yadda aka zabe ni don shiga takarar - ba zan yi karya ba, wannan na da muhimmanci a wajena.
Ko da yake ban ga alamun nasarar na zuwa a nan kusa ba. Na gamsu da samun nutsuwa. Watakila saboda na amince a wata rana zan iya samun nasarar," in ji shi.
Girmamar sana'arsa
Duk da rashin nasarar, Asake ya ce yana kallon kansa a matsayin wanda ya yi nasara, inda ya shiga takarar shejaru biyu kawai bayan yin shuhura a waka.
Ya ce "Ya kamata a fahimta: na isa wannan mataki a cikin shekaru biyu, amma tsawon shekaru ina ta aiki. Mutane na bin diddigin ranakun da ka yi nasara. Amma ba za su iya tuna lokacin da kake gwagwarmaya ba."
Rashin nasarar da mawakan Nijeriya suka yi inda 'yar Afika ta Kudu ta doke su, duk da farin jininsu, ya janyo bayyana ra'ayoyi da dama a shafukan sada zumunta na yanar gizo a tsakanin magoya baya daga kasashe daban-daban.
Wannan lamari ya sake tabbatar da hamayyar da ke tsakanin mawaƙan Nijeriya da Afirka ta Kudu ba z ata kawo karshe a nan kusa ba.