Daga Matthew Chan Piu
Ina da shekaru 43, na samu kaina a yanayi na tuna baya, ina tunanin lokacin da na mayar da hankali da sadaukar da kai ga fannin kida da waka wanda ya fi karfin ka kira shi da kida da waka kawai - hanya ce ta rayuwa gaba daya.
Salon waka da kida na Hip hop, da amonsa mai ratsa zukata da zallan karin sauti, ya fara shiga rayuwata sakamakon kyautar da daga baya ta sauya mu'amalata da kida da waka.
Kyauta ce daga wani da nake so da kauna, wanda ya fahimci yadda nake son kida da waka - mahaifiyata kenan.
Tare da murmushi mai shauki, ta miko min wata 'yar na'ura da kamfanin Sonic ya samar. Ashe ba ta sani ba zabin da ta yi na wakoki zai taka babbar rawa wajen sauya rayuwata.
Akwai rukunin wakoki guda biyu a kaset din da ta ba ni; NWA, wakokin "Straight Outta Compton" na 1988 NWA suka yi, da kuma wakokin "It Takes a Nation of Millions to Hold Us Back" na Public Enemy.
Bayanan bude wake na rukunin wakokin Public Enemy sun girgiza ni sosai, inda suka shiga tare da zama a ruhina ta yadda suka bar tabon da ba zai gogu ba.
Wadanda na fi kauna
Sai dai kuma, rukunin wakokin NWA masu ratsa zukata na "Straight Outta Compton" ne suka sanya nake kishingida a kan gadona, kunnuwana na saurarar wakokin.
Sautin da ya sake fayyace rukunin wakokin ya zama masu kara daukaka wakokin. Ya zama sai ka ce an fara wani juyin juya halin wakoki ne, kuma na zama daya daga cikin masu gudanar da wannan lamari.
Tun daga wannan lokaci, tafiyata a duniyar Hip Hop ta zama mai sanya ni bukatar ilimi da sauti. Na zama mai sauraren duk wani nau'i na waka da ya shigo hannuna, wanda hakan ya sanya na tara wakoki da dama, musamman wadanda aka yi a shekarun 1980 da kuma kyawawan shekarun 1990.
A yayin da na zurfafa cikin wannan fanni, sai na tsinci kaina a cikin kogin wakoki, sauti, kafiya da suke bayar da labarai, suke tayar da hankula da labaran rayuwa.
Ice Cube, tare da wakarsa ta 'razor-sharp wordplay, ya zama wanda ya shiga ya yi kane-kane a zuciyata, wanda yana daga mawaka biyar da na fi so da kauna.
Yare gama-gari
Yadda yake yin wakoki yana bayar da labaran da za ka dinga surantawa a zuciyarka, ya ja ra'ayi da hankulan mutane da dama da suka hada da ni, wanda hakan ya sanya mayar da wakokin Hip Hop su zama a kan gaba. Wani salo ne na bayar da labarai ga yankuna da al'adu daban-daban.
Duk da ya samo asali daga dubban kilomita a Amurka, hip hop na magana ga mutane a Afirka, a harshen Afirka da ba ruwan su da nisa.
Ta hanyar salon waken wadannan mawaka, mutum na jin ya kusanci abubuwan da suke fada - fasalin garuruwansu, gwagwarayarsu da mahukunta, burinsu a rayuwa da matsalolin da ke damun zukatansu.
Hip hop ya zama rumbun ajiye labaran rayuwar mutane, harshe gama-gari da dukkan mutane daga kowanne bangare suke fahimta.
Wannan abu na al'ada, wanda ya samo asali a al'umun da ake dannewa hakkoki, na da karfin hade kawunan zukatan da aka kuntatawa karkashin kafiya guda.
Warkar da ciwuka
Ba wai ya shafi kida da waka ba ne kawai, ya shafi gwagwarmaya, rayuwa da manufofin bai-daya don samar da duniya mafi kyau.
Wani abu makamancin hakan shi ne, hip hop ba wai nishadantarwa kawai yake yi ba, yana kawo sauyi a tsakanin al'umma, yana daga muryoyin da ba a jin su, kuma mudubi ne da ke bayyana gaskiyar yadda duniya take.
A lokutan damuwa, masu sha'ar hip hop na kunna wakokin da suka fi so don samun sanyin zuciya, su bayyana wani hali da kalmomi ba za su iya bayyana su ba.
Kafiya da hawa da saukar sautin hip hop na da wani salon dabarar bayar da waraka ga zuciya, warkar da ciwuka da sanya juriya.
A yayin da shekaru suka ja, hip hop ya zama mahadar abokai da kulla dangantaka a duniya.
A yanayin da na gani da idanuna, daga samun wakokin gambara sababbi, zuwa ga samun sabbin abokai, zuwa ga sauraron wakoki a lokacin harshen da ake magana da shi ya gaza, hip hop ya zama gadar da ta hada ni da wasu nahiyoyin.
A yayin da masoya hip hop suke kallon me zai zo a nan gaba, yana da muhimmanci a jaddada cewa labari ne na so da kauna da ya yadu daga zamani zuwa wani zamanin, kuma salon waken wata alama ce ta gwagwarmayar al'adu da suka yi shuhura a tarihi.
Ci-gaba da nuna so da kauna ga wanzuwar hip hop shaida ce da ke tabbatar da karfin wakoki wajen sauya rayuwar mutane, hada abota da kawar da kalubale.
Kamar yadda KRS-One ya fada "Wakar gambara wani abu ne da muke yi, hip hop kuma wabu ne da muke rayuwa da shi." Tabbas, hip hop ya fi karfin zama wani salon waka; hanyar rayuwa ce, alada ce, kuma mudubin rayuwar dan adam.
Jigon hadin mai kai karfi
Tun daga titunan Los Angeles zuwa na New York da ke da kai komon jama'a, hip hop ya zama hanyar bayyana abun da ke zukatan mutane da martanin sauran jama'a, inda yake cakuda salon sautin Afirka na gargajiya da sautukan zamani.
Wannan hadin gambizar wakoki da ya dace da juna na samar da habakar sauti, yana bayyana wahalar rayuwar Amurkawa 'yan asalin Afirka.
A matsayin matashi dan Afirka da ke ninkaya a kogin kafiya da sakokin hip hop, na gano ni ma ina tattare da irin bayanan da mawakan suke bayarwa na gwagwarmayarsu da ma ta al'ummunsu, sannan suna bayyana kulabalen da suke fuskanta yau da gobe, nasarori da burikan rayuwar matasan nahiyar Afirka.
Zamanin masoya
Ko mutum ya yi ta kai komo a duniyar wakokin Kwaito na Afirka ta Kudu da ke ratsa zukata, ko kuma ninkaya a kogin wakokin hip hop na Nijeriya, wannan salo ya zama matattarar hada kawuna waje guda. Yana sanya ilhama da jama'ar zamani daban-daban su tashi su amfani damar bambance-bambancen da ke tsakaninsu, suna bukukuwan karfi da yaduwar al'adun Afirka.
A karin sauti da jerin wakokin hip hop, ba wai salon waka kawai na fahimta ba, na gano nau'ukan sautin yankuna daban-daban, da suke hada matasan Afirka waje guda, suna karfafar su da ba su damar cika burinsu na rayuwa.
Watakila tun daruruwan shekaru da suka gabata hip hop ya bar nahiyarmu a siffar kidan ganga, kafiya da wakoki, sai aka sake haifar sa a New York a matsayin sabon salon sauti, amma har yanzu yana dauke da kwayoyin halittar asalin yankin da ya fito na Afirka.
A waen mutane da dama iri na da suka girma daal'adar hip hop, ya zama wata doguwar tafiya ta bude idanu, neman ilimi da bayar da labaran rayuwa.
A kowacce shekara da ke wuce wa, hip hp na ci gaba da habaka kamar wutar da ke ci ba kakkautawa, tana haskaka hanyar masoyan waka da za su zo a nan gaba.
Marubucin wannan makal, Matthew Chan-Piu, marubuci ne kuma mai shirya fina-finai da ke Kampala, Uganda.
Hattara: Ba dole ba ne ya zama ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.