Daga Charles Mgbolu
Magoya baya na taya murna ga mawaƙi Kwabena Ofei-Kwadey Nkrumah bayan da wata kafar yada labaran yankinsu ta sanar da ya samu nasarar ƙarar da ya kai gaban kotu yana kalubalantar Tarayyar Kwallon Kafa ta Afirka bisa amfani da waƙarsa ba tare da izininsa ba.
Kwabena da aka fi sani da sunan wakarsa ta Spiky, ya samu diyyar dala 250,000 a kotun kasuwanci ta Accra bayan ya kai CAF kara a 2019 bisa amfani da wakarsa ta 'Okomfo Anokye' wajen tallata Bayar da Kambi na gasar CAF ta 2018, in ji kafafen yada labarai a Ghana.
CAF ba su mayar da martani kan lamarin ba, amma ka'idodjin amfani a shafin yanar gizonta na bayyana cewar "suna girmama hakkin mallaka".
A wata tattaunawa da aka yi da Spiky a yanar gizo a 2019, ya ce a lokuta daban-daban ya rubuta wa CAF, ya kuma rubuta sakonni a shafukan sada zumunta na yanar gizo yana neman da a sauke waka da kidansa, sannan a biya shi diyya, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Spiky ya kara da cewar bidiyon tallan bikin sun kasance a yanar gizo har sai bayan da aka kammala bayar da kyaututtukan na CAF 2018 a watan Janairun 2019.
Bidiyon da ake rikici a kai na nuna hotunan 'yan wasa da aka nada don shiga gasar Lashe Kambi ta CAF 2018 bangaren dan wasan da ya i kowane.
An yada bidiyon a yanar gizo amatsayin tallata bikin bayar da kyaututtukan da aka yi a Dakar, Senagal.
Bidiyon da ya nuna 'yan wasan da aka zaba don shiga gasar, na da kidan Afirka wanda Spiky ya ce na wakarsa ta 'Okomfo Anokye' ne aka dauka ba tare d aizinins aba.
Ka'ida ta shida ta sharuddan aiki na CAF ta bayyana karara cewa "Idan ka yi amanna cewa an yi amfani da wani abu mallakinka a shafukan sadarwa na yanar gizo na CAF, to ka gabatarwa da CAF wadannan bayanai: suna, sunan karshe, adireshi, adireshin mail, nau'in kayanka da aka yi amfani da shi da kuma yadda aka yi amfanin (kwanan wata, lokaci da sauran su).
Duk da wadannan ka'idoji, Spiky ya yanke shawarar tunkarar kotu bayan ya gaza samun martani daga wajen CAF kan su sulhunta juna.
A ranar Laraba, Spiky ya fada wa kafar yada labarai ta Citinewsroom da ke Ghana cewa, "Wannan nasara ba tawa ni kadai ba ce; nasara ce. ga dukkan mawaka da matasan Ghana da suka yanke kauna da tsarin da ake kai."
Spiky ya sake yada sakon taya murna da babban mai rubutu a yanar gizo na Ghana Mac Jordan ya aike masa wand aya rubuta "Ina sara maka, @therealspiky, saboda gwagwarmayar da ka yi har zuwa karshe.
Wannan ya zama abin koyi da darasi ga dukkan masu kida da waka na Afirka kan su tsaya kan kare hakkin kayan da suka mallaka."
Okomfo Anokye, wani kida da waka na minti uku da saniya 15, ya fito a ranar 20 ga Yunin 2015 a mahajar Soundcloud ta sauraren kide-kide.