Mawakiyar gambarar Amurka Bia ta ce tana jin dadin wakokin Davido da Wizkid da Burna Boy

Daga Charles Mgbolu

A zamanin da aka fi ganin wakoki maimakon jin su, mawakiyar gambarar Amurka Bia, ta shaida wa taurariyar wakar kasar Trinidad Nicki Minaj a wata tataunawa da suka yi kai tsaye a shafin Instagram, cewar ba za ta iya gane mawakan Nijeriya Wizkid da Davido da kuma Burna Boy ba, amma ta san su kuma tana jin dadin wakokinsu.

Wannan ka iya zama wata alama da ke nuna yadda wakokinsu suka keta iyakar kasarsu.

A farkon wannan karnin, yawancin wakokin Nijeriya da na Afirka sukan shahara ne kawai a cikin kasashensu ko kuma a hada su da wasu wakoki a cikin nahiyar.

Wakoki daga mawakan Nijeriya irin su Tuface Idibia (African Queen, 2004) da DBanj (Fall in Love, 2008) da PSquare (Do Me, 2007), su ne misalan wakokin da suka ja hankulan mutane a wajen yankin, amma ba su yi girman da za ju ja hankalin ‘yan Afirka masoya wakoki da ke zama a wajen nahiyar ba.

Shekara goma da suka gabata, an ga cigaban nasarorin wakokin Afirka a wajen nahiyar, inda a kowace shekara ake kara samun wakokin da suka fi na shekarar da ta wuce karbuwa a duniya.

A halin yanzu wakokin Afirka sun fara samun lambar yabo ta Grammy.

Mawakan Ladysmith Black Mambazo daga Afirka ta Kudu sun samu lambar yabon wakar da aka fi so sau biyar.

Adadin ya karu da wadanda Angelique Kidjo (Benin) da Burna Boy suka samu a shekarar 2022 da 2021. DJ Black Coffee na Afirka ta Kudu ya samu lambar yabon a shekarar 2022.

Wadda ake ji kwanan nan, marubiciyar waka ‘yan Nijeriya Tems, ta zama taurariya a wajen ba da lambar bikin ba da lambar yabon a birnin Los Angeles a cikin watan Fabrairu,

Ta samu lambar yabo a wani bangare tare da masu wakar gambara ‘yan Amurka, Future da Drake kan wakarta mai suna Wait for You.

A da yawancin wakokin Nijeriya da na Afirka sukan shahara ne kawai a cikin kasashensu/Dbanj Twitter

Wizkid da Davido sun samu kasonsu na yabo a bikin karrama bakake masu nishadantarwa wato Black Entertainment (BET) Awards, inda suka samu lambobin yabo na wakar ta da fi kyau a Afirka da kuma wakar da ta fi shahara a kasashen duniya.

Wizkid ya kuma ya ja hankalin mutane a duniya a lokacin da ya doke Drake da Kanye West wajen samun lambar yabon ta bakin fatar da ya shahara a duniya a bikin ba da lambar yabo ta MOBO cikin shekarar 2021.

Shin mene ne yake kara fitar da baiwar ‘yan Afirka kuma yake sa su dade a cikin taurarin duniya?

Phiona Okumu, shugaban sashen wakoki na manhajar Spotify wadda jigo ce a harkar sayar waka ta intanet, yana da tabbacin cewar sautin Afirka da ya fita daban ya yi kargo a lokacin fasahar da ta dace.

"Fasaha ta yi matukar sauya abubuwan da ke kawo sauyi a harkar waka. A cikin gomman shekarun da suka wuce, rediyo ya kasance kafar da ta fi farin jini wajen sauraron waka da kuma sani game da sabbi da mawaka masu tasowa.

"A yau, raba murya ko bidiyo ta zama wata hanya mai karfi da mawaka ke amfani da ita wajen isar da wakokinsu," in ji ta a hirarta da TRT Afrika.

A shekara 2021, Wizkid ya sayar da dukkan tikiti 20,000 na filin taro na O2 Arena a Kudu maso gabashin Landan cikin minti 12, inda ya zama mawakin Afirka na farko da ya fara yin hakan, kuma ya saka shi cikin wadanda suka iya sayar da tikitin dakin taro na O2 Arena cikin minti 15.

Wadannan mawakan sun hada da Beyonce da the Spice Girls da Rihanna da The Rolling Stones da Monty Python da kuma Garry Barlow.

Wizkid ya taba samun lambar yabo a gasar karrama bakake masu nishadantarwa (BET) Awards/Wizkid Twitter

Ko ma babu baban dandalin, baiwar waka a cikin nahiyar na samun cigaba.

Marubuci kan harkar nishadi dan Ghana, Ameyaw Debrah, ya yi bayani kan abin da ya sa hakan.

"A yau za ka iya kasancewa a Ghana ka kuma dora wakarka kan intanet, kuma wani a Mexico zai iya samun wakar.

"Shafukan sada zumunta sun saukaka wa masoya waka su iya samun mawaka da wakokinsu kuma su yi zantukan da za su taimaka wajen fadada jin wadannan mawakan.

"Ingancin wakoki da bidiyoyin wakoki da kuma hadin gwiwa sun ba da tasu gudumawar," in ji shi a hirarsa da TRT Afrika.

Mai shirya waka dan Afirka ta Kudu Taffy Da Don, ya yarda cewar yadda sautin Afirka ya fita daban ya sa ya zarce sauran sautukan a kasancewa ko ina.

"Wakokin Afirka sun tace dukkan sautukan yammaci da na ketare daga sautukansu.

"A yanzu, sautin Afirka ne kawai. Kasancewarsa sautin Afirka kuma sauti mai jan hankali shi ya sa yake kara yawan fitarwa da kuma yawan jin sautin Afirka a dandalin duniya."

A yanzu da sautin Afirka ke kara samun karbuwa, shin za a bar masu hadin gwiwa a baya?

Daga Beyonce zuwa Justin Bieber da Ed Sheeran da Chris Brown, sanannun sunayen ketare sun hada kan da mawakin Nijeriya wajen fitar da wakoki.

Mawakin Amurka Omarion ya hada kai da Diamond Platnumz daga Tanzaniya yayin da kungiyar mawakan Kenya Sauti Soul sun yi waka da mawakin Amurka Indie Arie.

DJ Sidtrus na Hong Kong a bara ya ba da sanarwar cewar zai saka mawakan Nijeriya biyu, Yung Bos da Sultan Afrob, a wakarsa.

Ya fada wa kafafen yada labaran kasar cewar masoya waka a Asiya na shaukin salon waka da rawa na Afirka.

Marubucin Ghana, Ameyaw Debrah ya ce za ka iya dora wakarka a intanet daga Ghana kuma wani a Mexico ya same ta/Ameyaw Debrah Twitter

Neman wakokin Afirka ya karu sosai har ya kai ga wasu lokutan abubuwa na wuce goina da iri.

A cikin wantan Disamban 2022 turereniya da turmutsutsu ya sa masu shiri sun soke wakar da mawakin Nijeriya Asake zai yi a dakin taro na Brixton O2 Academy a Landan, wanda ya cika makil da masoya waka da suka kai 5,000.

Wadanda suka shirya wakar sun ba da sanarwa a kan dandali cewar wasu masoya waka 3,000 da suke waje sun balle kofa suna yunkurin shiga da karfin tuwo. Mutum biyu sun mutu a wannan lokacin.

Wani babban kamfanin shirya waka a Afirka, One Africa Music Fest, ya wallafa a Instagram cewar ya yi yarjejeniya da manyan mawakan Afirka kan za su zaga nahiyoyin Turai da Asiya da Ostireliya da arewaci da kuma Kudancin Amurka), don yin waka a sama da birane 100 a 2023.

Debrah, wadda ta ga tafiyar tun ba a san da ita ba zuwa lokacin da ta yi nasara, ta kasa boye mamakinta.

“Shekara 17 da suka wuce, da na fara ba da rahoto kan nishadi, ba kasafai ake jin dan Afirka na cewa shi yana son ya samu lambar yabo ta Grammy ba. Amma a yanzu sun gane cewar hakai zai yiwu, kuma suna fita neman ta."

Phiona tana ganin fasahar AI mai kama da tunanin mutun ne abu na gaba da zai sauya fasalin abubuwa a waka.

"Kayayyakin aiki irin su tsara bayanai da hanyar da komfuta ke bi don koyon tunani na mutum da kuma manhajar AI mai tunani tamkar mutum da ake samu a shafukan da ke sayar da sauti ko bidiyo a intanet, sun inganta tare da sauya yadda mawaka ke haduwa da masoyansu.

"Kuma hakan ya taimaka musu wajen gina sana’arsu da kuma samun yawan mabiya."

Yanzu lokacin kakar mawaka a Afirka ya wuce, lamarin da zai ba su hutun da suke bukata daga wakokin shagali da za a yi a makonni na karshe a shekarar 2022.

Za su koma kan hanya da kuma sudiyo don hada sautin Afirka wanda zai kasance waka mai dadi da kunnen duniya.

TRT Afrika