Daga Firmain Eric Mbadinga
A duk lokacin da ta karɓi na'urar magana, marubuciyar waƙe, mawallafiya kuma mai gabatar da waƙe a gaban jama'a, muryar Chi Margaret Edun, ƴar shekaru 25 da haihuwar, tana zarce karsashin bajintar da take nunawa.
Waƙe da zuben Margaret sun wuce a ce kalamai ne kawai da aka saƙa domin isar da da tunaninta da ra'ayinta; tana amfani da iya saƙa zancenta da kuma kyakkyawar mu'amalarta da mutane a matsayin wasu abubuwan samar da sauyi.
A matsayinta ta ɗaya daga cikin masu tasowa a fagen nuna bajintar adabin Cameroon, Margaret ta yi imanin cewa alhaki ne da ya rataya a wuyanta, ta yi amfani da fasaharta, ta jawo hankalin masu sauraronta kan adana kyawawan ɗabi'u da al'adun ƙasar da kuma watsi da ɗabi'ar kowa-tasa-ta-fishe-shi bisa haɗin kai da taimakekeniya.
Margaret tana sauke nauyin dake kanta na bayar da shawara da taimakon matasa a yankin Bamenda, da ke arewa maso yammacin Cameroon, ta hanyar hanyar ƙungiyarta The Literary Touch-THELIT.
A cikin shekaru uku da suka gabata, ƙungiyar THELIT tana horas da matasa rukuni rukuni ta fuskar lafazi da azancin zance, kamar waƙe da jawabi a bainar jama'a da kuma gabatar da waƙe a cikin mutane.
Hadafin shi ne a faɗaɗa basirarsu, da lalubo abin da zai zamo musu abin dogaro da Kai a fagen fasaha da kuma inganta shaksiyyarsu.
Basirar da Margaret ke da ita da kuma ƙwarewarta sun sa shirin horaswa na THELIT ya samu karɓuwa.
"Na samu kyaututtuka da dama, kuma an wallafa ayyukana a mujallun gida da waje. Har wa yau, na samu horo a kan wanzar da zaman lafiya, da kula da muhalli da kuma kuma dakatar da kalaman ɓatanci," ta sheda wa TRT Afrika.
Koyar da yadda za a yi tunani
Ƙasidar horaswar ba ta ƙunshi zaƙulo ƴan baiwa da kuma koya musu yadda za su gabatar da kansu ba ne kawai - har ila yau, tana ƙarfafa wa waɗanda ake horaswan su iya yin tunani mai zurfi kuma a bayyane, da yin nazari kan al'amuran al'umma kamar cin zarafin jinsi da yadda za a shawo kansu.

"Shirin ya ƙunshi duk wani abu game da jawabi a bainar jama'a, sadarwa,ƙagaggun labarai, aiki tare da shugabanci,aiki da hankali, tattaunawa da al'umma da kuma iya mu'amala da jama'a," a cewar Margaret.
Kawo yanzu,matasa 23 da ƙungiyar THELIT ta horas sun zama gawurtattun masu rubutu da karanto jawabi ko waƙe.
Har wa yau, an koyar da su kan yadda za su tunkari lamurran da suka shafi matsugunansu na kusa da na nesa.
A watan Satumban da ya gabata, ɗaya daga cikin tarurrukan da mashiryan suka ƙaddamar, ya mayar da hankali kan maudu'ai kamar kula da muhalli da kyaun da asalin Afrika ke da shi, da ganin kamewa da kuma ƙwarin guiwa.
Taron ya buƙaci waɗanda ake bai wa horaswar su tattauna kan waɗannan maudu'an, kafin su sarrafa su zuwa salon waƙe, daga nan su gabatar da su a gaban jama'a tare da karsashi da yaƙini.
Babu bambancin matakin karatu
Kwasakwasan, waɗanda kyauta ne kuma har ɗaliban da ba su kammala digirin farko ba za su iya halarta,za a iya amfani da shi domin dalilai na ƙwarewa, da ilimin da kuma neman waraka.
"Na koyi abubuwa da dama daga waɗannan tarurrukan da kuma yin nazarin ayyukan sanannun masu waƙe da marubuta. Hakan ya ba ni damar kyautata rubuce rubucena da kuma ƙara faɗin karance karancena," a cewar Blessing Ndfutu.
wani wanda ya ci gajiyar shirin na Margaret, yanzu yana iya rubuta waƙe gabansa gaɗi. Ƙungiyar THELIT na samun tallafi daga ɓangarori daban daban domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta.
Idan ba ƙungiyar gida kamar Xhuma África Association ba, Jami'ar Bamenda na bai wa Margaret aron harabarta domin ƙarfafa ayyukanta na wayar da kai, waɗanda tuni ana ganin tasirinsu.
"Za a iya auna tasirin shirin nawa ta hanyar sauyin ɗabi'un waɗanda suka halarci darussan namu. Da farko, wasu mahalartan sun ƙi sakewa sannan suna jin kunya kuma gabatar da kansu na musu matuƙar wuya.
Sannu a hankali, da ƙwarin guiwarsu ya ƙaru, sai suna iya bayyana kansu da baiwar da suke da ita, ɗaiɗaikunsu da kuma a ƙungiyance, Margaret ta sheda wa TRT Afrika.
"Da zarar sun samu horaswar, galibinsu sun zaƙu su bayyana fasaharsu a tarurruka daban daban. Saboda haka akwai gagarumin tasiri."
Gina fasahar rayuwa
Tsawon lokacin da Margaret ke ɗauka tana koyarwa,aƙalla, yana ɗaukar wata ɗaya. Amma tana ɗaukar isasshen lokaci ta bibiyi ɗaliban nata ɗaya bayan ɗaya, domin ta tabbatar sun koyi abin da ya keɓanta da su kuma sun raba.
"Na tuna, alal misali, abu mafi wahala da na taɓa fuskanta - wata ƙaramar yarinya da ta kasa gane ita wace ce kuma tana tsoron shiga jama'a. Na fahimci ta kasa shiga cikin mutane ta sake," Margaret ta tuno.
Tun kafin fara taron ƙarawa juna sani na waƙe da rubutu, Margaret na taimaka wa wannan ɗalibar, da ma wasu a rukunin, su fahimci cewa, maganin matsalar rashin sanin kai, ba ƙoƙarin koyi da kowa da kowa ba ne, illa mutum ya yi ƙoƙari ya gano sannan ya bayyana wata baiwa ta musamman tattare da shi.
Yayin da take ƙarfafa guiwa, bayar da horo da kuma kawo sauyi a rayuwar masu son koyi da ita, Margaret na karatun digiri na biyu a kan sadarwa da cigaba a Jami'ar Bamenda.
Tana shirin samar da wani ƙawance tare da cibiyoyin gwamnati da na ƴan kasuwa domin nemo kyakkyawar makoma ga ƴan'baiwa da take ganowa ko da kuma wasu ba su gano su ba.