Daga Fırmaın Erıc Mbadınga
Papa Seck, wanda ya taba yin rajista a matsayin matashin dan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Faransa Olympique Marseille Academy, bai taba tunanin zai hada kafadu da wasu daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a duniya ba.
Yana da burin zama ƙwararre, sai dai kamar yadda wasan kwallon kafa ta gada, nasarar dan wasa ba ta hannunsa baki daya.
Bullar annobar COVID-19 da kuma zaman kulle da aka yi a Faransa suka tilasta masa kawo karshen burinsa, sai dai hakan ya bashi damar kirkiro bidiyoyi a kafar TikTok - wani sauyi da ya kai shi ga shahara a duniya kuma ya samu gayyata zuwa manyan wasannin kwallon kafa a matsayin baƙo.
“Na kasance ina buga kwallon kafa. An haife ni a Marseille kuma a can na girma. Tun ina shekara hudu zuwa 15 nake wasa a kulob din OM (Olympique Marseille), sannan daga baya na canza kulob lokacin ina da shekara 20,'' a cewar Pape yayin hirar da TRT Afrika ta yi da shi.
Ya kara da cewa ''daga nan ne aka shiga kullen takaita yaduwar cutar COVID wanda ya yi sanadiyar dakatar da komai," in ji Pape Seck.
Daga wannan lokacin ne baiwarsa ta barkwanci ta fito fili, kuma ya samu kafa ta yada bidiyoyinsa cikin sauki inda masu kallo a fadin duniya suka fi mai da hankali sakamakon zaman kullen da ya samar.
Bidiyonsa sun jagoranci sauran kirkirar shirye-shirye da samari bakaken fata ke yi, wadanda suka dace da masu kallon da ke magana da harshen Faransanci a lokacin annobar.
Tushensa na harshen Faransancin Senegal ya ba da gudunmawa sosai wajen samun karuwar masu kallo.
“A lokacin da na fara, ba a kalla bidiyoyin da na kirkirosu da farko sosai ba, saboda ba a sanni ba, a cewar Pape
''Daga lokacin bullar COVID-19 na fara hada bidiyoyi masu ban dariya, dag nan ne abubuwa da anake yi suka fara yaduwa a kasar Faransa da Senegal da Mali da Belgium da yahiyar Afirka gabi daya, "in ji Pape, wanda ya tattara ra'ayoyin mutane da kuma alamar son abun da yake yi sama da miliyan 100 a shafukansa na intanet daban-daban.
Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsayin mai kunya, ya amince cewa ya matukar mamakin yadda ya shahara a kafar TikTok, yana mai cewa "dawowarsa" duniyar kwallon kafa ta zo ne a lokacin gasar kwallon kafa ta Afirka (Afcon) a shekarar 2021 a Kamaru.
Bidiyonsa a gasar, a lokacin da aka ware na tattaunawa da wasu daga cikin 'yan wasan da suka halarta, da kuma samun damar shiga dakunan canja kaya na 'yan wasan ya kara masa mabiya masu son kwallon kafa zuwa shafinsa na TikTok.
"Dukkanin bidiyon gasar Afcon da na daura a kafar sun sa na samu gagarumar nasara, inda a kalla wasu har sau miliyan uku a cikin kankanin lokaci," in ji shi.
Nasarar da ya samu sakamakon bidiyon gasar yada ta kafar TikTok ya kai ga gayyatar da ya samu a hukumance don halartar taron ba da lambar yabo ta CAF a shekarar 2023 a birnin Marrakech na Moroko.
Kai tsaye ya kalli yadda aka karrama 'yan wasan Nijeriya Victor Osimhen da Asisat Oshoala wadanda suka lashe kyautar gwarzon 'yan wasan Afirka na 2023 a fagen mata da maza.
Kazalika Pape ya halarci taron bikin Ballon d'Or guda biyu na baya-bayan nan, inda ya cika alkawarin da ya yi wa mahaifinsa wanda kasance babban masoyin wasan kwallon kafa.
“Daya daga cikin Hotunan da nake alfahari da su, shine wanda na dauka tare da mahaifina kusa da Kwallon Zinare, da gaskiya ne hoton da na yaɗa shi ne wanda nake ni kadai, amma a zahiri wanda na yi da mahaifina shi ne mafi muhimmanci a gare ni . Kullum ina tare da mahaifina.
"Duk da cewa ban yi nasara a kwallon kafa a matsayina na dan wasa ba, amma a ko yaushe ina son faranta wa mahaifina rai," kamar yadda Pape ya shaida wa TRT Afrika.
Pape ya danganta nasararsa a kan TikTok ga inganci bidiyonsa da kuma kirkirar shirye-shiryen barkwanci da yake yaɗawa.
Salon gajerun bidiyoyinsa da kuma wasu lokutan yadda yake sharhi ne suka kara masa armashi, inda ake iya ganinsa tare da ƙwararrun 'yan wasa kwallon kafa kamar Erling Haaland da Sébastien Haller da Sadio Mane da Jude Bellingham da kuma Vinícius Júnior da dai sauransu.
Ga wanda ya koya wa kansa daukar faifan bidiyo da kuma shirya shi tun yana da shekaru 12, shaharar da Pape ya yi ba ƙaraman nasara ba ce.
A yanzu haka yana daukar horo kan wani kwas na haɗa sauti mai bidiyo a Cibiyar d'Études des Sciences et Techniques de l'information a Jami'ar Cheikh Anta Diop da ke Dakar na kasar Senegal.
"Dole ne mutum ya yarda da mafarki da burinsa, sannan ya yarda da kansa kuma kada ya yi kasa a gwiwa," a cewar shawarar da Pape ya bai wa sauran matasa kamar sa.