Oluwadare: Mai zane-zane ɗan Najeriya ya sake maimaita wa masu sha'awar zane-zane da suka gundure su da salo iri ɗaya

Oluwadare: Mai zane-zane ɗan Najeriya ya sake maimaita wa masu sha'awar zane-zane da suka gundure su da salo iri ɗaya

Oluwadare ya ƙware wajen fasahar sarrafa zane-zane, wanda galibi ya ƙunshi azanci domin ya bunƙasa baiwarsa.
Mai zane-zanen surar abu na zahiri Oluwadare Samson ya ce gundurar masu sha'awar zane zane da salon iri ɗaya kodayaushe zai iya daƙile cigaban mai zane zane.Photo: Oluwadare

Daga Pauline Odhiambo

Mai zane-zane ɗan ƙasar Faransa ya ce fasaha na buƙatar ƙarfin hali. Wannan haka yake a wajen mai zane zane ɗan Najeriya Oluwadare Kolawole Samson wanda ya jure wa sauye sauye a yadda yake gabatar da zanensa.

Oluwadare ya ƙware wajen fasahar sarrafa zane zane, wanda galibi ya ƙunshi azanci domin ya bunƙasa baiwarsa da basirarsa ta zane zane.

"Maimaita salo iri ɗaya a aikin zane zane zai iya gundura, masamman a wajen masu sha'awar zane zane, waɗanda suke shauƙin ganin abubuwa daban daban," mai zane zanen surar abubuwa na zahiri na wannan zamanin ya sheda wa TRT Afrika.

"Gundurar masu sha'awar zane zane da salo iri ɗaya tawaya ce ga bunƙasar mai zane zane."

Zane zanen surar abu na zahiri ya ƙunshi aikin zane zane na zamani da ya jiɓanci abubuwan duniya na zahiri, musamman surar bil adama.

Zane-zanen surar abu na zahiri na nufin zane zanen zamani da ya jiɓanci abubuwan duniya na zahiri. Photo: Oluwadare

Flower motifs Zanen fure

Daga kallon zane-zanen Oluwadare, ka san sha'awar da yake da ita a kan zanen fure a bayyane take.

Furanni masu launuka gwanin sha'awa suna bayyana a galibin farfajiyar zane-zanensa. "Ina matuƙar ƙaunar fure," ɗan shekaru 34 ya bayyana. "Na gwada zanen fure na wani lokaci kafin na sake sauya shi sannan na gwada wani abu daban."

“Amma ko da nake aikin zane-zanen fure, na tabbatar na sassauya kamanninsu, sannan na yi amfani da launuka daban daban don kawai na sa su ci gaba da ɗaukar hankali da kuma jaddada sabuntarsu," ya ƙara da faɗa.

Wasu nau'o'i na al'adarsa ta Yarbawa su ma suna bayyana a aikin zane zanensa.

Fatar mutanen da yake zanawa a zanensa na mai tana bayyana da launi mai duhu don nuna asalinsu na ƴan Afrika

Tsagar fuska

Ɗaya daga cikin zane zanensa mai take, 'Duk batu ne kan kyau ' ya nuna wata mata ta yi kitso mai kama da kambun sarauta. Duk da akwai ƙuruciya a jikinta, idonta ya bayyana tsufa da ke ɓoye shekarunta.

A kuncin matar akwai wasu fitattun zane guda biyu da ba su ragi kyaunta da komai ba.

Wasu nau'ika na al'adar Oluwadare ta yarbanci sun bayyana a zane zanensa Photo: Oluwadare

"Mata da dama a inda na tashi a Ibadan suna da waɗannan tsagar fuskar, abubuwan da wani ɓangare ne al'ada sannan har ila yau suna nuna banbance banbance tsakanin al'adu." ɗan asalin jihar Ondon ya bayyana.

A cewar cibiyar bincike ta JSTOR, manyan tsaga, galibi a kowane kunci ko goshi dangi da al'ummomi ne ke yi wa ƴaƴa, yawancin lokaci, a matsayin tsagar tantance asalin mutum.

"Kowace tsagar fuska ta bambanta da wata kuma tana nuni da ƙabila, gari dangi ko zuriyar wanda aka yi wa," inji Oluwadare.

Amma al'adar ta shuɗe lokacin da gwamnatin tarayya a shekarar 2003 ta ce guntule wani sashi na jikin mutum ne sannan ta haramta al'adar.

Waɗanda suke da tsagar fuska a halin yanzu sune mutane na ƙarshe da suke da su - abin da ya zaburar da masu aikin zane zane kamar Oluwadare su sake farfaɗo da al'adar ta hanyar zane zane.

Ƴar'baƙa Kyakkyawa

Saɓanin wasu masu zane zane, Oluwadare ya fi son zana surar mace.

"Mata wani muhimmin bangaren rayuwarmu ce. Suna bayar da rayuwa ne a zahiri ta hanyar ɗaukar rai a mahaifarsu na tsawon wata tara, wannan kawai ya sa sun zama na musamman," mai zane zanen ya furta.

Galibin zane zanen oluwadare suna yaba wa siffofi na musamman na Matar Afrika ne. Photo: Oluwadare

Sai kuma aka dace, zane zanen Oluwadare mai take 'Untamed Mother' ya nuna wata tsohuwa wacce salon kitsota da daidaituwarta suka yi kama da alamar shahararriyar bishiyar nan ta rayuwa wacce ƙabilu daban daban a faɗin duniya suka cusa a fasaharsu da al'adarsu.

Sauran zane zanensa da yawa sun haɗa da 'The Jamilah’ and ‘Goal Getter' suna da jigo na jinjina ga siffofin musamman na matan Afrika.

"Babban hadafin aikina shi ne na tallata kyakkyawar baƙar fatar matan Afrika ta hanyar salon kitsonsu da kuma tsarin rayuwarsu," mai zanen surar bil adama na zahirin ya bayyana.

"Zanena na aika saƙon karfafa guiwa ta hanyar nuna adon matan Afrika da kuma wasu bangarorin zamantakewar rayuwarsu."

"The Golden Blubber' wani zane ne da ke yin bayani kan rashin adalci. Photo: Oluwadare

Ci-da-gumi irin na mulkin mallaka

Wasu daga cikin zane zanen Oluwadare sun tattauna batutuwan wariyar launin fata. Yana ɗaukar shi kimanin makwanni biyu ya kammala kowanne daga zane zanensa.

Zanensa mai take ‘Love Cares Less’ ya yi nuni da shaƙuwar ƙauna tsakanin mutane.

"Babu wani abu wai shi wariyar launin fata a soyayya," ya faɗa, yana ƙarawa da cewa an halicce mu ne domin mu ƙaunaci juna, ko ta halin ƙaƙa. Saboda haka, a dena nuna wariyar launin fata, soyayya ta tsakani da Allah babu ruwanta da wannan.

A wani zanen mai take 'The Golden Blubber’, an ga wani mutum da wani tafkeken tabo a gadon bayansa.

"Abin da ya assasa wannan zanen shi ne tarihin bauta lokacin da aka ci da gumin baƙar fata ƙarƙashin tsarin mulkin mallaka,"Oluwadare ya faɗa wa TRT Afrika. "Irin wancan uƙubar ba abu da za a iya mantawa ba ne ko da tsakanin da yawa daga cikinmu da aka haifa bayan zamanin mulkin mallaka.

"Love Cares Less" yana nuna soyayya tsakanin mutane. Photo: Oluwadare

Oluwadare na tura zanen a shafukansa na dandalin sada zumunta aka sayar da shi nan take. An sayar da ƙarin zane zanensa kan dubban daloli a kasuwar duniya.

"Wani abokina wanda shi ma mai zane zane ne ya shawarce ni da kar na sayar da shi, amma a wancan lokacin,ina buƙatar kuɗin na sake zuba shi a harkar aikin zane zanena," ya tuno.

"Na yi yi ainihin nadamar sayar da shi, kuma a wani lokacin, na yi tunanin na sake zana wani irinsa sak, amma ba abu mai sauƙi ba ne maimaita kamarsa.

'The Jamilah' zane ne da ke karrama al'adu da kyaun Afirka Photo: Oluwadare

Amma hakan bai hana shi samun gamsuwa da zanensa a kai a kai ba.

"Na fi farin ciki idan ina zane zane. Ina matuƙar ƙaunar abin da nake yi kuma wannan kaɗai shi ke ƙarfafa ni musamman idan ina fama da ƙalubale,"inji mai zane zanen wanda ya kwashe shekara Goma yana zane zane a matsayin sana'a.

"Na ji daɗi da na kasance a matsayin da zan faɗi fahimtata tare da sauran duniya."

Shawararsa ga masu zane zane masu tasowa: "Babu wani dabo tattare da shi, kawai ka ci gaba da yin shi," ya faɗa. "Za a iya jin maganar wata iri, amma yi akai akai shi ne abu mafi muhimmanci."

TRT Afrika