Kayan da Belinda Yesum ke samarwa sun samu karbuwa a kasarta Kamaru.

Belinda Yesum tana karar da kusan dukkan lokacinta wajen tunanin sabon nau'in saka da za ta yi, wand akuma zai dace da kalar da za ta saka shi.

Tare da kayan sakarta na kwarashi da ulu mai nau'ika daban-daban, tana zama a shagonta da ke Yaounde, babban birnin Kamaru, ta dinga sabbin kayayyaki, sannan ta tallata su a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

Tabbas, kayan sawa, takalman ulu da mashimfidin teburan cin abinci, duk na nan a shafinta na Faceboolk kuma suna an hankalin mutane. A yayin wata tattaunawa da TRT Afirka, Belinda ta ce tana aikin samar da 'yan kunnaye.

Belinda ta ce "Na sayi wasu 'yan kunne kuma ina sake saka su don ba su wani sal na musamman. Za a iya sarrafa wadannan 'yan kunnaye zuwa nau'i kala-kala, irin yadda ka ga dama."

Belinda Yesum ta ce tafiyarta ta sana'ar saka da dinki na cike da kalubale da yawa.

Ayyukan Belinda sun samu yabo, karbuwa da bibiya a shafukan sada zumunta. Amma kuma sana'ar saka ba ita ta yi niyyar ta zama sana'arta ba, idan da za ta yi duba da me ta karanta a jam'ia da irin horon da ta samu.

Ta gama jami'a a 2010 a sashen banki da sarrafa kudade daga Jami'ar Buea da ke kudu maso-yammacin Kamaru. Amma tsawon shekaru hudu ba ta samu aikin yi ba.

"Na je wajen wata intabiyu da na halarta an bayyana ni ce na fi kowa hazaka, amma a karshe kuma ban samu aikin ba, watakila saboda ban bi diddigi da bayar da wasu 'yan abubuwa ba.

"Wannan abu ne na bakinciki, sanin cewa ka cancanci ka samu aiki, kai ne ka fi dacewa da aikin, wand aya yi maka intabiyu ya fada maka hakan, amma a karshe kuma ba ka samu ba." in ji ta, a tattaunawar da ta yi da TRT Afirka.

Daga baya ta samu ai a karon farko, amma kuma ba ta dade tana yi ba saboda wasu dalilai.

Kayan yara na sakawa na daga abubuwan da suka fi tafiya.

Samun jarin fara wannan aiki na bamuwa da kalubale a yankin da mutane kadan ne kadai ke da buri irin wannan.

Belinda ta ci gaba da bayanin cewa "Da fari na sha wahala sosai. Kafin na samu kudin sayen ingantattun kayayyaki, sannan babu wani ta'mako da tallafi da na samu."

Mai sana'ar saka ta fadawa TRT Afirka sirrin da ke tattare da saka na samun waraka da tafiyar da gajiya, musamman a lokacin da take son tafiyar da damuwarta.

Ta ce "Yin wannan na taimaka min sosai wajen tafiyarwa da maganin damuwa. Na tsara nau'i, sannan na dinka su, na mayar da su na gaske na bukatar mayar da hankali waje guda. A lokacin da kake saka, ba ka tunanin komai sai ita."

A yayin da ake ta yabon kayan yara kanana da na ado da take samarwa a shafukan sada zumunta, tana korafi kan ba ta samun masaya da yawa, da kuma yadda wasu sai dai su tambayi farashi kawai su kara gaba.

A yayin da take murmushi da bayar da bayanai game da sana'ar tata, Belinda ta kuma bayyana cewa "Don saka kayan sawa na ciki na mata guda biyu, wanda sai da na sayi ulu da yawa kuma kala daban-daban,na caje su saifa 5,000, dinka wannan abu na duakar kwanaki a kalla hudu."

Ana nuna bukatar kayan sawa na mata sosai.

Belinda na fatan samun kudade da yawa zai taimaka mata wajen inganta sana'arta da kuma samun isassun kudade.

Belinda ta kuma ce "Abun da ne yi sana'a ce. Na kan dauki makonni kafin na samar da wasu kayan, idan kuma ba su yi kyau ba, sai na sake daga farko. Amma a wasu lokutan kwastomomi ba sa fahimtar wahalar da aka sha idan aka fada musu farashi."

Tana kuma bayar da horo ga mutane a fannin saka dari bisa dari, wanda a wajen ta sana'a ce ta kaka da kakanni da bai kamata a ce ta bace ba.

TRT Afrika