Daga Pauline Odhiambo
Neman abin da zai ba ka ƙwarin gwiwa ka yi zane na kama da cika kwandon siyayya da abubuwa masu kyau na rayuwa da ake gani a kullum ga mai zanen na Rwanda Benhamin Niyomugabo, kasuwa ita ce abin da ke jan hankalinsa ya yi zane.
A kasuwar Mutangana ta Kigali, yana ganin rayuwa na tafiya ta ɓangarorin da suka haɗa da damarmaki da sa rai da juriya da nasara da gwagwarmaya.
Kowace rumfa da kowane shago na cike da mutane da ke shiga kasuwar. Babban burin Niyomugabo shi ne ya ƙara ɗaga darajar yadda za a fassara zanensa, da kuma yin zanen da ke tafiya da rayuwa, da kuma bayar da wata fassara.
Ɗaya daga cikin zane-zanensa na baya-bayan nan mai taken “Bike Brothers”, ya samo asali ne daga lura da sa ido kan wasu daga cikin waɗanda rayuwarsu ta ta’allaƙa ne da kasuwar.
“Wasu daga cikin masu shagunan ba su da matsala wurin bayar da labarin rayuwarsu ta yau da kullum a kasuwar,” kamar yadda mai zanen ɗan shekara 23 ya shaida wa TRT Afrika.
“Yanayin aikinsu na da kyau kuma yana bayar da ƙwarin gwiwa, kuma ina son zanena ya nuna hakan.”
Taken ya samo asali ne daga ɗaya daga cikin hanyar sufuri da masu shagunan suka fi amfani da ita a Mutangana da sauran ‘yan kasuwannin da ke cikin birni.
Akasarinsu na amfani da kekuna domin sufurin kayayyakin gona da sauran kayayyaki zuwa cikin kasuwar da kuma wajenta.
Mu’amala mai kyau
Yanayin mu’amalar da Niyomugabo ke yi da masu shagunan ta ta’allaƙa ne kan aminci.
Yana girmama ra’ayinsu haka kuma suna ba shi goyon baya dangane da aikinsa na zane, duba da yadda suke ganin yana zane game da yanayin rayuwarsu.
Kamar yadda shafin Art Story ya bayyana, irin zanen da Niyomugabo yake yi na realism yanayin zane ne da aka soma irinsa tun daga shekarun 1960 zuwa farkon shekarun 1970.
Irin wannan zanen ya ƙunshi zanen rayuwar yau da kullum fiye kuma babban burin irin wannan zanen shi ne fito da abin da ke bayyane ba na tunani ba.
“Akwai ma’aikatan kasuwa da dama waɗanda suka bar abin da suke yi daga cikin lokacinsu domin yin tattaunawa mai kyau da ni da kuma ba ni labaransu,” kamar yadda Niyomugabo ya shaida wa TRT Afrika.
“Abin da nake so a kowane lokaci shi ne na nuna yanayin rayuwarsu a zane.
Ƙarfi ya haɗu da kyau
Ana yawan samun mata a zane-zanen Niyomugabo, da labaransu, da kuma ƙarfin da suke amfani da shi wurin gwagwarmayar yau da kullum.
“Zana mata aiki ne mai daraja, sakamakon suna da ƙarfin kawo jin daɗi ga duk wani wanda ke tare da su,” in ji shi.
Haka kuma mai zanen ɗan asalin Kigali na son yin zane irin wanda ke ɗaukaka baƙar fata.
Haka kuma ɗaya daga cikin fasaharsa akwai addu’a, wadda ke taimaka masa fito da irin abin da ke cikin zuciyarsa ta hanyar zane.
“Zanen da nake yi yana fito da yadda nake ji sakamakon yana fito da ainahin abin da ke cikin zuciyata idan ina zane,” in ji shi.
“Yanayin da nake na addu’a na taimaka mani fito da shawarwari iri-iri, waɗanda nake zazzanawa kafin na saka masa launi.”
Bayar da ƙwarin gwiwa ga masu tasowa
Akwai zane-zane da dama na Niyomugabo waɗanda masu tara zane-zane suka ɗauka domin baje-kolinsu.
Ya yi aiki da wuraren ajiyar zane-zane da dama daga ciki har da Mitochondria da ke Houston a Texas da kuma Fortysecond Space da ke Rwanda.
Ya bayyana dalilin da ya sa yake samun haɓaka a sana’arsa da da “ci gaba da koyo” inda yake ci gaba da koyo daga sauran masu zane.
“Na samu ƙwarin gwiwata daga manya irin su Vincent van Gogh da Leonardo da Vinci da wasu da dama,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Ina so na yi zanen da zai bai wa yara masu tasowa ƙwarin gwiwa,” in ji shi.