Dabino yana cikin 'ya'yan itace masu ɗauke da sikari da ya kai kashi 60-65%. / Hoto: Getty

Daga Mazhun Idris

Dabino ɗan itace ce mai zaƙi wanda ke fitowa a bishiyar dabino, wadda bishiya ce mai juriya da ƙarfin rai. Ana lissafa dabino cikin bishiyoyi mafi tsufa da ɗan'adam ya sani, kuma dabino ba shi da tsada wajen saye.

Saboda daɗinsa, da sinadaren gina jiki, da kuma tasirin magani da yake da shi, mutane da dama suna amfani da dabino a faɗin duniya.

Dabino kayan marmari ne da yake da farin jini wajen al'ummar Musulman duniya, musamman a lokacin azumin Ramadana.

Akwai nau'ukan dabino da dama a da ake samu a ƙasashen duniya. / Photo: Instagram/@haulat_home_kitchen

Dabino na da muhimmanci a addinance wajen Musulmi, sakamakon cewa a ambace shi cikin kayan marmari na Aljanna.

"Annabi sallahu alaihi wasallama ya ce a buɗe baki da dabino lokacin shan-ruwa," a cewar Malama Haulatu Zakariya Yakubu, Malama a Sashen Ilimin Musulunci a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a Nijeriya, da take magana da TRT Afrika.

Dabino yana da albarka, kuma ɗan itace ne da ke farfaɗo da jijiyoyi da ƙara kuzari a jikin ɗan'adam.

Nau'o'in dabino a wata kasuwa da ke Makka.

Malama Haulatu ta ambato ayoyin Ƙur'ani da ke nuni da amfanin dabino ga lafiyar mutum, da kuma tasirinsa kan lafiyar mata masu juna-biyu.

Malamar jami'ar da ke koyar da ilimin Musulunci, ta kuma kawo hadisi, wanda ke nuna abin da Annabi Muhammadu SAW ya koyar.

"Idan ɗayanku zai buɗe baki bayan azumi, to ya fara da dabino saboda yana da albarka. Idan bai samu ba, to ya fara da ruwa saboda tsarkinsa," (Tirmizi, Hadisi mai lamba 696).

Ana tauna dabino ko a jiƙa shi, ko a niƙa shi a sha. Hoto: Instagram/@haulat_home_kitchen

Haka nan kuma, malaman Musulunci suna yin nuna da cewa an so mai buɗe-baki ya ci adadin mara na dabino, kamar ɗaya, ko uku, ko biyar.

A ɓangaren girki kuwa, ana zuba dabino a nono, da smoothie, da kunun zaƙi, waɗannan nau'ukan abin-sha ne da da ake yi a Nijeriya.

Malama Haulatu wadda ita ma tana haɗa abubuwan-sha da dabino, ta ce, "Ba wai shi kansa dabinon ba, ana kuma amfani da ƙwallon dabino da aka soya aka niƙa sannan a sha shi kamar kofi, amma sai dai shi ba shi da sinadarin caffein."

TRT Afrika