Masana kiwon lafiya a Nijeriya sun yi kira ga masu azumtar watan Ramadan a wannan shekarar su yawaita shan ruwa sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi da ka iya haifar da cututtuka saboda rashin wadataccen ruwa a jiki, musamman ga masu aikin ƙarfi a wuraren da zafin rana ya yi yawa.
A wata sanarwa da Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta fitar a shafinta na X a watan Fabrairu, ta yi hasashen cewa yankin arewacin ƙasar zai fuskanci tsananin zafin da ya zarta maki 41 a ma'aunin salshiyas, sannan sama da maki 39 a yankin kudancin ƙasar.
Azumin bana ya riski al'ummar Musulmai a jihohin Nijeriya a irin su Kano da Sokoto da Zamfara da Babban Birnin Tarayya cikin tsananin zafi, kuma tuni likitoci kamar su Dakta Muhammad Dauda Haroon na Asibitin Koyarwa na ATBU da ke jihar Bauchi, suka ce an fara kai musu marasa lafiya da tsananin zafin ya yi wa illa, waɗanda kuma suka ɗauki azumi.
''Irin wannan yanayin ya fi ƙamari kan masu aikin ƙarfi, ko waɗanda suke gudanar da sana'o'insu cikin yanayin tsananin rana,'' in ji Dakta Muhammad Dauda Haroon.
''Idan ruwa ya ragu a jikin ɗan'adam zai dinga jin bakinsa yana yawan bushewa, sannan yawan fitsarinsa zai ragu ya kuma yi duhu, hakan na iya haifar da matsalolin rashin ƙarfin jiki da ciwon kai da tashin zuciya da amai da dai sauransu'', kamar yadda likitan ya shaida wa TRT Afrika Hausa.
Da yake magana da TRT Afrika Hausa, Sheik Muhammad Bin Uthman, wani malamin addinin Musulunci da ke birnin Kano na arewacin Nijeriya, ya shawarci Musulmai su sha ruwa sosai a lokacin yin sahur da buda-baki.
Ya ce "Wannan zai rage musu tsananin ƙishi ruwan da ka iya shafar walwalarsu a yayin da suke azumi a tsananin zafi”.
Ya ƙara da cewa, “A yanayi na matukar takura, ya halatta Musulmi ya karya azuminsa idan zai iya zamowa haɗari ga lafiya ko rayuka, musamman idan karya azumin shi ne kaɗai mafita a gare shi”.
Dakta Muhammad ya bayyana cewa akwai yiwuwar ɓarkewar cututtuka masu alaƙa da zafi da kuma ƙarancin ruwa a jikin ɗan'adam waɗanda suka haɗa da cutar sanƙarau da ƙyanda har da suma a wasu lokutan.