Kamfanin wakar na Mavin ya samar da zaratan mawaka fasihai da suka yi zarra a duniya. Hoto: Mavin Records      

Daga

Charles Mgbolu

Zaratan mawaka da suka yi shuhura a duniya irin su Tiwa Savage, da Rema da Aura Star wadda ta shiga Gasar Grammy duk yaran kamfanin ne.

Sai dai Tiwa Savage ta sanar da ficewarta daga kamfanin, inda ta koma kamfanin mawaka na Amurka, Universal Music Group a Mayun 2019.

Yanzu haka akwai fitattun mawaka matasa da tauraronsu ke haskawa a yanzu irin su Johny Drill, da marubucin waka Crayon da Magixx da Boy Spyce da Teddy da yanzu haka suke karkashin kamfanin mai dimbin masoya a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.

Don Jazzy fitaccen forodusan waka ne a nahiyar Afirka. Hoto: Don Jazzy

A ranar 8 ga Mayun 2012 ce Michael Collins Ajereh wanda aka fi sani da sunan Don Jazzy ya assasa kamfanin na Mavin Records.

Kafa kamfanin ke da wuta, sai ya zama matattara fasihan mawakan Nijeriya, inda matasan mawaka ke samun damar nuna fasaharsu a duniya.

Bayan kamfanin mawaka na Mo Hits Record, wanda shi Don Jazzy din da D'banj suka assasa ya durkushe a shekarar 2012, sai shi Don Jazzy din ya kafa sabon kamfani da niyyar daga darajar nau'in wakar Afrobeats da yake kauna, inda ya dauko matasan mawaka irin su Wande Coal da Tiwa Savage da Dija da da Reekado Banks da Korede Bello a sabon kamfanin.

Da farko Don Jazzy ya hada hannu da D'Banj ne wajen assasa kamfanin Mohits Record kafin ya assasa Marvin Records daga bisani. Hoto: Dbanj/Instagram

Duk da cewa dukkan wadanda aka fara kamfanin wakar da su, yanzu sun raba gari, har yanzu kamfanin na cigaba samun daukaka.

Haka kuma kamfanin na aiki tare da wasu fasihan daga ko'ina a nahiyar Afirka.

A shekarar 2017, fitaccen mawakin Tanzania, Diamond Platnumz ya yi waka tare da mawakiyar kamfanin Tiwa Savage a wata wakarsa mai suna 'Fire' da ta yi shuhura sosai, sannan mawakin kamfanin Rema, ya yi waka tare da fitaccen mawakin Kamaru, Yseult a wakar 'wine'.

A shafin Instagram, Don Jazzy ya wallafa alamar godiya domin murna cika shekara 12 din, sannan tsohon mawakin kamfanin Reekado Banks ya rubuta, ‘’Muna godiya da damar da aka ba mu.’’

Mavin’s record bai tsaya wajen horar da matasan mawaka ba kawai, yana cigaba da aikin da su domin tallata su a duniya.

Fitaccen mawakin Rema yaron kamfanin na Mavin Records ne.

Shirin 'The Mavin Future Five' wani shiri ne da aka tsara domin horar da matasan mawaka, sannan a hada su da kwararru domin bunkasa fasaharsu.

A watan Fabrailun 2024, Kamfanin Universal Music Group (UMG), ya sanar da shiga yarjejeniyar miliyoyin Daloli da Kamfanin Mavin, inda aka bayyana kamfanin a matsayin Mavin Global, domin nuna cewa matsayin kamfanin ya kai matakin duniya.

TRT Afrika