Mai kamun kifi Camille Dimale ya shafe shekaru biyu yana amfani da wannan kwale-kwalen roba, kuma ya ce ya gamsu  - photo - trt afrika

Daga Anne Nzouankeu

TRT AFRIKA,Yaoundé

A gabar tekun Londji a Kamaru, a kusa da jerin kwale-kwalen katako na gargajiya, akwai kuma kwale-kwalen da aka yi da kwalabe na roba.

Mai kamun kifi Camille Dimale ya shafe shekaru biyu yana amfani da wannan kwale-kwalen roba, kuma ya ce ya gamsu.

"Ba shi da nauyi kuma mai sauƙi a gare ni don amfani da shi saboda wani lokaci ina zuwa kamun kifi ni kaɗai. Don haka zan iya ɗauka cikin sauƙi, in kai shi cikin ruwa, in dinga motsa shi ba tare da buƙatar taimako ba. Ba ya lalacewa cikin sauƙi haka,'' in ji Dimale

Ya fi sauƙin tattali, ya fi inganci. Ba na jin tsoron cewa zai karye ko ya tsage ko kuma ya yi yoyo. Haƙiƙa yana da amfani sosai,” in ji Dimale.

Kwale-kwalen kwalaben robar ya fi sauƙin tattali, ya fi inganci. - photo - trt afrika

Kamaru na samar da sharar kusan tan miliyan shida a kowace shekara, gami da tan 600,000 na robobi.

A kan sabunta wata sharar, amma wata kamar su robobi waɗanda ba za a iya lalata su ba, ana watsi da su barkatai inda suke gurɓata muhalli da ruwa.

Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Madiba and Nature ta yanke shawarar rage wannan gurɓatar muhallu ta hanyar sabunta su don sake amfani da su. Takan tattara waɗannan kwalabe, ta wanke su, a ɗaure su wuri guda, ta ƙera kwale-kwale ta bai wa masunta.

Shugaban ƙungiyar mai zaman kanta, Ismaël Essomè, wani injiniyan kula da muhalli, ya bayyana cewa ya ƙirƙiri wannan abin ne a lokacin da yake neman mafita don tsaftace bakin teku yayin da yake taimakon masunta.

Kwale-kwalen kwalebn robar na bai wa masunta damar zuwa wuraren da ba zai iya isa da kwale-kwalen da aka saba amfani da shi ba - photo - trt afrika

"Madiba and Nature ta yanke shawarar ƙera kwale-kwale da kwalaben robobi don tallafa wa kamun kifi, saboda kamun kifi na ɗaya daga cikin manyan ayyukan tattalin arziki a Kamaru," in ji shi.

"Kwale-kwalen da aka yi da kwalabe na robobi yana da arha, ba shi da tsada fiye da kwale-kwalen da aka yi da itace, kuma yana da mai sauƙin tattalu, sannan yana bai wa masunta damar zuwa wuraren da ba zai iya isa da kwale-kwalen da aka saba amfani da shi ba," in ji Essomè.

Kwale-kwalen kwalaben roba na Kamaru. - photo - trt afrika

Kungiyar mai zaman kanta ta ce tana karɓar kusan tan uku zuwa biyar na kwalaben roba duk wata. Ana amfani da wasu daga ciki don ƙera kwale-kwale, ɗayan kuma ana sayar da shi ga sauran abokan hulɗa da suke sabuntawa don sake yin amfani da su.

TRT Afrika