Ana kallon DJ Maphorisa a matsayin wanda ya tallata kidan Amapiano a duniya. Hoto: DJ Maphorisa a Instagram.      

DJ Maphorisa yana cikin makada masu fasaha sosai a Afirka ta Kudu.

Haka kuma fasihin mawaki ne, sannan marubucin waka, wanda masoyansa na gidi suke kira da "Sarkin kidar Amapiano", wadda salon kida ce mai tashe a kasar.

Asalin sunansa Themba Sonnyboy Sekowe, wanda aka haifa a 15 ga Nuwamban 1987 a garin Soshanguve da ke Afirka ta Kudu. Mahaifinsa dan Nijeriya ne, amma mahaifiyarsa 'yar Afirka ta Kudu ce.

Ya taso ne a cikin mawaka a gidansu; mahaifiyarsa wadda aka fi sani da Mama Maphorisa mawakiyar yabo ce, baffansa kuma yana cikin kungiyar mawakan yabo na Kiristanci na Soweto Gospel Choir.

DJ Maphorisa ya taso ne a gidan mawaka. Hoto: DJ Maphorisa a Facebook.

Da yake bayyanawa a wata tattaunawar da aka yi da shi a shekarar 2018, DJ Maphorisa ya ce tasowarsa a gidan mawaka ta taimaka wajen saukaka masa harkar, sannan ya ce ya taso ne yana koyon amfani da na'ukan kayayyakin kida a gidansu, wanda hakan ya sa ya kware cikin kankanin lokaci, har ya fara fice tun yana karami.

Tun yana dan yaro, Maphorisa ya fara halartar kananan taruka, da ya kai shekara 17, sai ya yanke shawarar barin makaranta...saboda yana bukatar isasshen lokacin da zai cika burinsa.

Sai dai iyayen shi ba su amince masa ba, amma daga baya DJ Maphorisa ya samu nasara har suke alfahari da shi.

Ana kallon DJ Maphorisa a matsayin wanda ya kawo sauyi wajen amfani da amapiano domin kida, inda yake amfani da shi wajen kirkirar kade-kade da suka yi shuhura sosai.

DJ Maphorisa yana cikin fitattun masu kida da sunansu ke amo a duniya. Hoto: DJ Maphorisa

Ya fara samun daukaka ne a shekarar 2013, lokacin da shi da abokansa aikinsa Magikizolo suka yi kidar fitacciyar wakar Khona.

Wakar Khona ce ta lashes Gwarzuwar Wakar taron karrama mawaka na Africa Music Awards wato MTV na 2014. A shekarar 2016, ya sake shiga cikin makadan wakar One Dance na mawakin gambarar Amurka, Drake, wadda ta yadu a duniya.

Wakar One Dance na cikin fitattun wakokin shekarar 2016, kuma ta samu lambar yabon platinum - wadda babbar lambar yabon ce a masana'antar wakoki- a sama da kasashe 10 a cikin Afirka da wajen Afirka.

Ta kuma zama gwarzuwar waka a akalla kasashe 15. Ita ce wakar da aka fi sauraro a tarihin wakokin da aka saurara a manhajar Spotify a Amurka.

Daga bisani DJ Maphorisa ya yi kidar wasu fitattun wakokin a Afirka da sauransu. Haka kuma shi ya yi kidar wakar Wizkid mai suna Soweto Baby da ita ma ta samu karbuwa.

DJ Maphorisa yana karbar kusan Dala 4,000 a duk taron nishadin da ya halarta, sannan ya samu karramawa da yawa, ciki har da Gwarzon Makidin 2023 na bikin SoundCity MVP Awards.

Har yanzu DJ Maphorisa bai da aure, amma yana da yarinya mai shekara 15 mai suna Lesidi.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince