Jones ya lashe kambin Emmy da Tony da dama. / Hoto: Reuters

Shahararru a harkar fina-finai na jimamin mutuwar James Earl Jones, wanda aka yi amfani da muryarsa a shirin "Star of the Wars" da ya mutu a ranar Litinin yana da shekara 93.

Muryar Jones, ta kuma fito a matsayin muryar King Mufasa a shirin "The Lion King" na tashar Disney, kuma mutum ne da ya yi shuhura a sana'ar tasa.

A tsawon sama da shekaru 60 ya yi aiki da manyan jaruman fina-finai, ciki har da Stanley Kubrick a shirinsa na 1964 mai suna 'Dr. Strangelove' da ke habaici game da yakin cacar baki.

Ya kuma taka rawa a fim din "Conan The Barbarian" na Arnold Schwarzenegger da shirin da Kevin Costner ya shirya a 1989 mai suna "Field of Dremas".

'Taka muhimmiyar rawa'

Sakamakon irin rawar da ya taka a manyan fina-finai ne ya sanya shi zama sanannen mutum a ko ina.

Jones ne wanda ya sanya shuhurar "Star Wars", har da a lokacin da ya bayyana wa Luke Skywalker - wand amatashi Mark Hamil ya fito a matsayin jarumi inda ya ce - "I'm your father.' (Ni ne mahaifinka)

A ranar Litinin Hamii ya yi rubutu a shafukan sada zumunta tare da bayar da sanarwar mutuwar Jones, yana cewa kawai "Ka kwanta a kabarinka lafiya baba" tare da alamar karyayyiyar zuciya.

Kewa

Jarumin "Rustin", Coleman Domingo ya rubuta a shfin sadarwa na yanar gizo cewa Jones "kwararren sana'armu".

"Muna tare da kai. Ka huta lafiya a yanzu. Ka yi mana iya kokarinka."

Lydia Cornell, wanda shirinta na "Bloodtine" da aka shirya a 1982 ya kasance mai kalubalantar Jones ya ce "Kai a'a!! Na kasa yarda da labarin nan!! Na zaci zai rayu har abada."

"Na ji dadin aiki tare da shi. Mutum mai karamci, da kankan da kai. Ya koya min yadda zan yi amfani da muryata."

"Selma", daraktar shirin Ava DuVernay ta yada hotunan Jones, ta kuma rubuta sakon ta'aziyya da jimami.

'Kyakkyawan aiki'

"Mun gode saboda yadda ka nuna mana yadda za mu san kanmu. Kawunanmu da suke a rikice, sanin mutuncin kanmu, da murmushinmu, da bacin ranmu. Kwararren iki. Kyautar da aka nuna wa kowa ta hanya mai kyau. Fatan albarka a lokacin da ka fara wannan tafiya."

Tare da wani bidiyon Jones da aka dauka a 1974 fim din 'Claudine', ta yi kira ga magoya baya da su kalli shirin matukar ba su yi ba a baya.

Ta rubuta "Yadda Mr. Jones yake kuka a wannan fim din ya zamar min hoto a fim mafi sanya tunani da wani bakar fata ya fito a cikin fina-finai. Kar ku rasa shi. Ya ba mu gudunmowa sosai,"

Jarumar shirin "The Help" Octavia Spencer ya yada hoto marar kala na Jones, tare da akon ta'aziyya da ya tunatar da rawar da ya taka a "Star Wars".

Ta rubuta "Ba wani kalami da zai iya bayyana irin rawar da ya taka da tasirin da ya yi kan fina-finai."

"Muryarsa da basirarsa za su zama abin tunawa a koyaushe. Ina aike wa da sakon nuna so da kauna ga iyalnsa, abokai da magoya baya da ba za su kirgu ba."

TRT Afrika