AKA ya yi nasarar cin kyaututtuka da dama kafin rasuwarsa. / Hoto: AKA

Daga Charles Mgbolu

A ranar Lahadi 10 ga watan Fabrairu, yan Afirka ta Kudu da masoya suka tuna da mawaƙin gambarar nan na Afirka ta Kudu wato AKA bayan ya cika shekara guda da rasuwa.

A ranar 11 ga watan Fabrairun 2023, masoyansa suka tashi da labari mai razanarwa kan cewa AKA, wanda sunansa na asali Kiernan Forbes ya rasu, bayan an harbe shi tare da abokinsa Chef Tebello Motsoane, wanda abokinsa ne a lokacin da suke hanyar zuwa wani wurin cin abinci a birnin Durban na Afirka ta Kudu.

Ƴan sandan Afirka ta Kudu sun ce wasu ƴan bindiga biyu ne suka buɗe musu wuta a kusa da kusa.

A shafukan sada zumunta, abokansa da masoyansa sun rinƙa aikawa da saƙon tunawa da shi dangane da irin nasarorin da ya samu da kuma tasirinsa a rayuwarsu.

"Ubangiji ya ja kwanan AKA! Ubangiji ya ja kwanan MEGACY #RIPAKA ❤️" kamar yadda @Nandi_Madida, budurwar AKA ta wallafa wadda ita ma mawaƙiya ce ƴar Afirka ta Kudu kuma ƴar fim.

Mau'du'in da aka rinƙa tattaunawa na #RIPAKA ya ja ra'ayi jama'a a ranar, inda aka rinƙa saka hotuna da bidiyoyin iyalai da abokansa a lokacin yana raye.

Da dama sun bayyana shi a matsayin gwarzo, musamman dangane da waƙoƙin da ya yi marasa gushewa.

Shi ma abokin AKA wato Tebello Motsoane an tuna da shi, inda mahaifinsa ya shaida wa wata kafar watsa labarai ta ƙasar kan cewa mahaifiyar Tebello ta rasu a bara sakamakon bugun zuciyar da ta yi fama da shi saboda ta kasa jure rashin.

Tebello Motsoane ya shahara a wurin girki. / Hoto: Tebello Motsoane

Tun bayan mutuwar AKA, waƙoƙinsa sun yi matuƙar suna inda suka samu kyaututtuka da dama a 2023.

Waƙar da AKA ya yi shi kaɗai ta "Lemons (Lemonade)” wadda a ciki akwai Nasty C da "Company" ta yi suna matuƙa, da "Dangerous", "Prada da "Mbuzi".

Haka kuma an karrama AKA a gasar BET Hip Hop. A watan Satumbar bara, 'Yan sandan Afirka ta Kudu sun sanar da gano makamin da aka yi amfani da shi wajen bindige mawaƙin da kuma motar da maharan suka yi amfani da ita. Sun sha alwashin ci gaba da neman wadanda suka kashe shi.

Sai dai bayan shekara ɗaya da kashe mawaƙin, babu wanda aka kama.

Hakan ya sa magoya bayansa sun karaya, kuma mutuwarsa ta kara zafi. Za su iya samun dangana ne kawai a cikin kiɗansa, da kuma abubuwan da ya bari na rayuwa.

TRT Afrika