Ngema fitaccen makidi ne kuma mai koyar da rawa. Hoto: l Mbongeni Ngema       

Daga Charles Mgbolu

Ana cigaba da aikawa da sakon ta'aziyar rasuwar fitaccen mawakin Afirka ta Kudu, Mbongeni Ngema, wanda ya rasu a wani hadarin mota a birnin Lusikisiki da ke Gabashin Cape a ranar Laraba yana dan shekara 68.

Ngema fitaccen marubucin wakoki ne, mai kida, mai koyar da rawa, furodusa sannan kuma darakta. An fi sanin shi a matsayin wanda ya shirya fim din Sarafina wanda ya karade duniya.

"Ina mika ta'aziyata ga iyalai, abokai da sauran masoya fitaccen mawakinmu mai kokarin nuna al'adunmu… Yadda yake nuna gwagwarmayar da muka sha wajen kwato 'yancinmu cikin kwarewa ya taimakawa wajen kara nuna darajar wadanda aka danne wa hakki, tare da kara fallasa irin girman zaluncin da aka musu," kamar Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya wallafa a shafukan sadarwa.

'Yan sandan Afirka ta Kudu sun bayyana cewa ba su hakikance asalin musabbabin hadarin ba, wanda ya auku a ranar Laraba da misalin karfe 4:30 na yamma, sannan suka kara da cewa za su zurfafa bincike.

Da fim dinsa na Sarafina kadai sai da ya samu shiga Gasar Tony Awards a matakai guda biyar daban-daban, sannan ya shiga Gasar Grammy ta duniya.

Ngema fasinja ne a cikin motar da ta yi hatsari. Hoto: Mbongeni Ngema

Fim din na Sarafina ya samu karbuwa matuka, inda fim din ya shiga Amurka da Turai da Austereliya da Japan, sannan daga bisa aka amince da shi a cikin finafinan tarihi.

Fitaccen mai koyar da rawa na Afirka ta Kudu, wanda ya yi aiki tare da Ngema a fim din Sarafina mai suna Somizi Mhlongo ya bayyana shi a matsayin, "Mutum mai matukar basira."

"Wannan mutuwar ta matukar girgiza ni matuka. Maigidana ya tafi. Mutumin nan, shi ne sanadiyar kwarewata. Shi ne mutumin da ya fahimtar da ni muhimmancin aiki da lokaci, ya sa nake matukar mayar da hankali a wajen aiki," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Shi ma Ministan Al'adu na Afirka ta Kudu, Zizi Kodawa ya bayyana mamacin a matsayin daya daga cikin fitattun makadan da suke alfahari da su a kasar.

"Afirka ta Kudu ta rasa daya daga cikin fitattun maruta wakokinta, makadi sannan darakta. Ayyukan Dokta Mbongeni Ngema sun karade Afirka ta Kudu da ma duniya baki daya," inji shi a wani rubutu da ya yi a shafuka sadarwa.

Shi ma fitaccen jarumin Afirka ta Kudu, Sello Make KaNcube ya aike da ta'aziyarsa.

Wasu daga cikin fitattun wakokin Ngema da suka yi shuhura sun hada da Woza Albert, Township Fever da ya yi a 1990, wadda ya samu kambun Grammy da ita da Mama (1995), Asinamali (1996), Maria Maria (1997) da The Zulu – The Musical (1999) da 1906 Bhambada da The Freedom Fighter da The House of Shaka (2005), da kuma The Lion of the East (2006).

TRT Afrika